Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya na tunanin komawa gonarsa da ke Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina don ya ci gaba da noma da kiwo
  • Buhari ya yi wannan furucin ne a Istanbul a kasar Turkiyya, a ofishin jakadancin Najeriya inda aka shirya masa bikin zagayowar shekarunsa
  • A cewar Buhari, zai yi iyakar kokarinsa wurin bunkasa Najeriya da neman ci gabanta har lokacin da zai mika ragamar mulki a shekarar 2023 ya yi, sannan ya kama gabansa

Kasar Turkiyya - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Kara karanta wannan

Ba zan daina muku aiki ba har sai ranar da na sauka a 2023: Buhari a jawabin cikarsa shekaru 79

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare
Buhari ya ce zai koma gonarsa a Daura da zarar ya kammala wa'adin mulkinsa a 2023. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.

An hada cake din da kalolin Najeriya

A cewar kakakin shugaban kasan, Garba Shehu, shugaban kasa ya yanka kek din da aka yi da kalolin Najeriya, kalar kore da fari yayin da ministan harkokin kasar waje, Geoffrey Onyeama ya yi bayani a maimakon sauran ministoci.

A bangaren Buhari kuwa cewa ya yi zai yi wa Najeriya iyakar iyawarsa har ranar da zai sauka daga mulki, sannan ya mika ragamar mulki ga magajinsa sannan ya koma gonarsa don ci gaba da noma da kiwo.

Kamar yadda ya ce:

“Na yi tunanin ba za a yi duk wadannan abubuwan ba tun da na yi nesa da Abuja. Har Guards Brigade sun rubuta abubuwan da su ke son yi a wannan ranar. Yanzu na zo nan kun shirya wannan duk da ina nesa da gida.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

“Ina jiran ganin shekarar 2023 lokacin da zan kammala mulkina, don in koma garinmu don ci gaba da tafiyar da gonata. Zan yi iyakar kokarina don ganin ci gaban kasata da mutanen cikinta kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.”

Shugaba Buhari ya sha wankasa sanye da kwat

Daily Trust ta bayyana yadda ya fito a shigarsa ta kwat har cikin dakin taro. Shugaban kasa Buhari ya hadu da wakilan Najeriya inda su ka jeru rike da kek din mai kalar Najeriya.

Taron jama’ar duk su ka fara cewa, 'Barka da zagayowar ranar haihuwarka, Shugaban kasa.'

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

A wani labarin, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari sarauta a Daura, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Na Alfahari Da Buhari, In Ji Kakakin Majalisar Wakilai, Gbajabiamila

Yusuf, wanda shine da namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel