Da Dumi-Dumi: Mutane da yawa sun mutu yayin da wani abu ya fashe a kauyen jihar Neja

Da Dumi-Dumi: Mutane da yawa sun mutu yayin da wani abu ya fashe a kauyen jihar Neja

  • Wasu abubuwan fashe wa sun fashe a kauyen Galadima - Kogo a jihar Neja, lamarin ya yi sanadin rasa rayuka da dama
  • Rahoto ya nuna cewa Nakiyoyin sun tashi ne awanni kaɗan bayan harin yan bindiga a kauyuka uku na yankin Shiroro
  • Har zuwa yanzun ba'a san adadin mutanen da suka mutu ba domin babu mai shiga yankin gudun abinda ka iya zuwa ya dawo

Niger - Wani abun fashewa da ake tsammanin yan bindiga ne suka ɗana shi ya tashi a ƙauyen Galadima-Kogo, karamar hukumar Shiroro, jihar Neja.

Jaridar Daily trust ta rahoto cewa fashewar ta auku ne awanni kaɗan bayan yan bindiga sun farmaki kauyuka uku, dake da nisan mitoci ƙalilan daga Galadima-Kogo.

Bayanan adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya yi wahala a halin yanzun da muke kawo muku wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da kansila da wasu mutane 8 a Sokoto

Yan ta'adda
Da Dumi-Dumi: Mutane da yawa sun mutu yayin da wani abu ya fashe a kauyen jihar Neja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Amma wani Sani Abubakar, na kungiyar matasan Shiroro, ya shaida wa manema labarai cewa da yuwuwar mutane da yawan gaske sun mutu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin zantawa da Channels TV, Abubakar ya ce:

"Mutane sun shiga cikin matsanciyar damuwa a yankunan da yan ta'adda ke yawan kai hari saboda tashin Nakiyar da ya auku."
"Fashewar Bam ko wani abu makamancin haka sabon abu ne a yankunan kuma bai saba faruwa ba, zamu alaƙanta haka da wasan yara da gwamnati ta ɗauki matsalar tsaro."

Mutum nawa suka rasa rayukansu?

Har zuwa yanzun ba'a san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, domin ba bu mai iya shiga yankin sabida tsoron hatsarin da ka iya aukuwa ba.

Yan ta'adda na cigaba da cin karen su babu babbaka a wasu yankunan karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, mutane na cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaba Buhari Ya Baro Brussels Domin Koma Wa Aso Rock

A wani labarin na daban kuma Yan sanda sun dakile mummunan harin yan bindiga a kan hanyar Kaduna-Abuja

Tawagar yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari sun kwashi kashin su a hannun yan sanda a kan hanyar Kaduna-Abuja.

Kakakin yan sandan Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce yan sanda sun dakile nufin yan bindiga, sun kwato makamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel