An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

  • Bayan korarsa daga aikin yan sanda, wani mutumi ya cigaba da sanya kayan hukuma yana yawo a gari
  • Jami'an yan sanda sun yi ram da shi lokacin da ya suka ga yana guduwa yayinda suka kusancesa
  • Kaakin hukumar yan sandan jihar ta ce za'a gurfanar da shi a kotu idan aka kammala bincike.

Abeokuta - Hukumar yan sandan jihar Ogun ta damke wani mutumin dan shekara 38, mai suna, Akinyemi Thomas, kan laifin ikirarin zama dan sanda.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ta bayyana hakan a jawabin ta saki a Abeokuta, birnin jihar.

Oyeyemi tace an damke mutumin ranar Alhamis, rahoton TVCNews.

CP na yansanda
An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta:

"An damke mutumin ne lokacin da yan sandan yankin Shagamu suke gudanar da sinitiri tare da DPO CSP Godwin Idehai."
"Sun hango mutumin sanye da kayan sarki karkashin gadar titin Legas-Ibadan."
"Yadda ya tsargu yasa yan sandan suka fara zarginsa kuma suka tsayar da shi don yi masa tambayoyi. Motar yan sandan na tsayawa ya tsere da gudu. Sai aka kure masa gud aka kamashi."
"Yayinda aka turke yi, ya bayyana cewa shi tsohon dan sanda ne amma yana amfani da kayan wajen damfarar jama'a."

Ta kara da cewa za'a gurfanar da shi a kotu idan aka kammala bincike.

An kama wata mata mai shekaru 30 da ta ƙware wurin siyayya da jabun N1,000 a kasuwa

A wani labarin kuwa, rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kama wata mata mai shekaru 30, Bola Agbedimu bayan ta kashe kudaden bogi a kasuwar Kila da ke karamar hukumar Odeda a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Wacce ake zargin ta zo hannun hukuma bayan mutane sun kai korafin ta hedkwatar ‘yan sanda da ke Odeda akan kashe kudaden bogin a kasuwanni.

Vanguard ta bayyana yadda kakakin ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya sanar da manema labarai a Abeokuta ranar Juma’a cewa an kai wa DPO din ofishin ‘yan sandan Odede, CSP Femi Olabode korafi, inda ya tura jami’an sa kasuwar daga nan suka yi ram da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel