Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

  • Tsohon kwamishinan labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Danmaliki ya koka kan cewa wasu na barazana ga rayuwarsa
  • Danmaliki ya ce wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun farmaki gidansa da ke garin Gusau, inda suka harba bindiga a lokacin da ya je Abuja
  • Jigon na APC ya aika rubutaciyyar wasika zuwa ga hukumomin yan sanda da na DSS a jihar a kan su yi bincike don ceto rayuwarsa da ta iyalinsa daga fadawa halaka

Zamfara - Tsohon kwamishinan labarai na jihar Zamfara kuma jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alhaji Ibrahim Danmaliki, ya koka a kan barazanar da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suke yi masa.

Danmaliki ya bayyana hakan a wata wasika wanda ya kai rahoton lamarin ga hukumar yan sandan jihar da daraktan hukumar DSS na jihar wanda aka gabatar ga manema labarai a Gusau, a ranar Litinin, 13 ga watan Fabrairu, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa
Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Wasikar ta ce:

“Wannan don sanar da ku game da yadda wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka harba harsashi a gidana, kusa da cibiyar lafiya ta tarayya, Gusau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu, 2022, da misalin karfe 10 na safe iyalina sun kira ni, lokacin ina Abuja, sannan suka sanar dani abun bakin cikin cewa an ji karar harbi a harabar gidana.
“Daga baya sai aka ga harsashi mai motsi a gidana sannan harbin ya shiga ta rufin gidan.
“Don haka ina kira ga rundunar yan sandan jihar da ofishin na DSS na jihar da su dauki matakin gaggawa kan wannan lamarin, saboda a ceci rayuwata da ta iyalina.”

A halin da ake ciki, da yake tabbatar da lamarin, jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce kwamishinan yan sanda, Ayuba Elkanah ya riga ya samu korafin daga tsohon kwamishinan.

Kara karanta wannan

'Dan-karen wahalar mai ya sa farashin fetur ya tashi da kusan 150%, lita ta kai har N400

Shehu ya kara da cewa kwamishinan yan sanda ya riga ya yi umurnin bincike a kan lamarin, rahoton Daily Nigerian.

Ana barazana ga rayuwata don na ki yarda a tsige mataimakin gwamna – Dan majalisar Zamfara

A gefe guda, dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Salihu Usman, ya bayyana cewa ya gudu ya bar jihar saboda barazanar da gwamnatin jihar ke yi masa don ya ki goyon bayan yunkurin tsige mataimakin gwamna.

Mista Usman shine dan majalisa daya tilo da ya rage a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar bayan dukka sauran sun bi Gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar da ta gabata.

Dan majalisar ya ki halartan zaman karshe da majalisar ta yi a makon da ya kamata wanda a lokacin ne yan majalisa 18 daga cikin 22 suka jefa kuri’un tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahadi Ali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel