Najeriya ta yi rashi: Daya cikin wadanda suka rubuta taken Najeriya ya rasu

Najeriya ta yi rashi: Daya cikin wadanda suka rubuta taken Najeriya ya rasu

  • An jefa Najeriya cikin jimami da makoki bayan rasuwar daya daga cikin wadanda suka rubuta taken Najeriya, Farfesa Babatunde Ogunnaike.
  • Ogunnaike, yana dan shekara 21, ya rubuta galibin kalmomin da suka hada da dango biyu na taken Najeriya a shekarar 1977.
  • Farfesan wanda haifaffen Ijebu Igbo ne a jihar Ogun na daya daga cikin ‘yan Najeriya biyar da aka hada kalamansu da hazakarsu wajen tattara taken

Daya daga cikin marubuta biyar na taken kasar Najeriya 'National Anthem' Farfesa Babatunde Ogunnaike ya riga mu gidan gaskiya. Ya rasu yana da shekaru 65.

An haifi Ogunnaike a ranar 26 ga Maris, 1956 kuma ya fito ne daga garin Ijebu Igbo ta jihar Ogun.

Wani fitaccen masanin ilimi a Najeriya kuma mawallafi, Gbenro Adegbola ne ya tabbatar da mutuwarsa, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari da abokan harkallarsa 6

Farfesa Babatunde ya rasu
Najeriya ta yi rashi: Daya cikin wadanda suka rubuta taken Najeriya ya rasu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kadan daga tarihinsa

A cewar Adegbola, Ogunnaike ya fito a matsayin daya daga cikin biyar, wadanda aka hada kalmominsu da jimlolinsu a cikin taken kasa.

Sauran sun hada da: John A. Ilechukwu, Eme Etim Akpan, Sota Omoigui, da P.O. Aderibigbe.

Ogunnaike ya yi karatu a Jami’ar Legas a digirinsa na farko, inda ya kammala digirin farko a fannin injiniyancin sinadarai a shekarar 1976.

Ya ci gaba da karatunsa, inda ya samu digiri na biyu a fannin kididdiga daga Jami'ar Wisconsin-Madison da digirin digirgir a fannin injiniyancin sinadarai duk dai a jami'ar ta Wisconsin-Madison a 1981.

Ogunnaike injiniyan bincike ne a rukunin kula da tsari na Kamfanin Shell a Houston, Texas daga 1981 zuwa 1982.

Ya yi aiki a matsayin mai bincike na DuPont kuma ya kasance kwararren mai ba da shawara ga kamfanoni da yawa ciki har da Gore, PPG Industries, da Corning Inc.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

Ya shiga harkar koyarwa inda ya fara karantarwa a Jami'ar Delaware a 2002 kuma an nada shi zuwa Farfesa na William L. Friendship of Chemical Engineering a 2008.

Ogunnaike ya zama shugaban riko na Kwalejin Injiniyanci a Jami’ar Delaware tun daga watan Yulin 2011 an kuma nada shi shugaban Kwalejin Injiniyanci tun 1 ga Yuli, 2013.

Ya yi ritaya a matsayin shugaban tsangaya a ranar 1 ga Oktoba, 2018 amma ya ci gaba da harkar koyarwa har mutuwarsa a kasar Amurka.

Gudunmawarsa a taken Najeriya

Farfesa ya ba da gudunawar ayoyi biyu daga cikin ayoyin taken Najeriya, kamar yadda Gbénró Adégbolá ya fada a shafinsa na Twitter.

Felicia Adebola, marubuciyar da ta rubuta taken alkawarin Najeriya; 'National Pledge' ta rasu

A rahotonmu na baya, kunji cewa, farfesa Felicia Adebola Adedoyin, marubuciyar taken alkawarin kasa na Najeriya, ta mutu a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Biki bidiri: Gwamnati ta aurar da tubabbun yan gidan magajiya a Bauchi

Marigayiya Adedoyin wanda aka haifa a ranar 6 ga Nuwamba 1938 itace ta biyu cikin yara shida kuma Gimbiya daga Gidan Iji Ruling na Saki dake karamar hukumar Saki ta Yamma, yankin Oke Ogun na jihar Oyo.

Masaniyar a fannin ilimi, ta samu digirinta na uku a shekarar 1981 daga Jami’ar Legas, Nairaland ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel