Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

  • Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya shawarci tsofaffin da su ba matasa fili domin su zama shugananni a zaben 2023 mai zuwa
  • A cewar Obasanjo, lokaci ya yi da matasa za su kula da harkokin kasar nan ganin halin da ake ciki a yanzu
  • Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a matsayinsa na shugaban wani taro da wata fitacciyar gidauniya ta shirya

Najeriya - Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu ya yi kira ga tsofaffin ‘yan Najeriya da su ba da dama ga matasa masu tasowa wajen gina Najeriya.

A cewarsa, maimakon su tsaya takara, ya kamata tsofaffi su hada kai da matasa tare da samar musu da ilimi da gogewar da ake bukata domin kawo sauyi ga kasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisa ta tsige mataimakin shugaba, wasu yan majalisu biyu sun yi murabus

Obasanjo ga shawarci tsoffin 'yan takara
Mulki ba naku bane: Obasanjo ya gargadi tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obasanjo a lokacin da yake magana a taron shekara-shekara na gidauniyar Murtala Muhammed Foundation na 2022 mai taken, ‘Beyond Boko Haram: Addressing insurgency, banditry, and kidnapping across Nigeria’.

A yayin taron, babban bako, gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya ce lokacin yana makarantar sakandare a shekarun da marigayi Murtala Mohammed ya jagoranci al’amuran kasar nan, kamar yadda SaharaReporters ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obasanjo a wani martani ga kalaman Fayemi ya ce:

"Muna bukatar samun hadin gwiwa tsakanin tsararraki. Fayemi yace yana makarantar firamare lokacin Murtala-Obasanjo ke can. Don haka, idan tsararrakin Murtala-Obasanjo suna takara da kai a matsayin gwamna to lallai akwai damuwa.
“Ya kamata tsararrakin Murtala-Obasanjo su koma gefe. Ko wanne irin gogewa da ilimin da kuke da shi, muna iya ba ku, kuma muna iya ba masu zuwa a bayanku, ta yadda duk abin da kuke da shi ku ma mika shi ga masu zuwa a baya kada su fara gasa da ku sai dai ma ku sami damar yin abin da zai sa ku gyara Najeriya ta fi kyau fiye da yadda kuka same ta."

Kara karanta wannan

Obasanjo: Abin Da Ƴan Boko Haram Suka Faɗa Min A Lokacin Da Muka Haɗu

Obasanjo ya kuma dora alhakin rashin tsaro a kasar kan samun makamai barkatai tun bayan yakin basasar Najeriya.

2023: Ta yuwu Najeriya ta samu 'yan takara 2 marasa amfani idan aka dubi yanki, Sanusi

A wani labarin, Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya ce alanta mulkin shugaban kasa ga yanki zai iya sa kasar nan ta kare da 'yan takara biyu marasa amfani a 2023.

A yayin jawabi a Arise TV a ranar Juma'a, Sanusi ya ce sau da yawa ya na kushe duk wata tattaunawa da za a yi kan yankin da ya dace ya samar da shugaban kasa, TheCable ta ruwaito.

Manyan jam'iyyu biyu na kasar nan na APC da PDP suna ta cece-kuce kan yankin da zai samar da shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.