Yadda Ɗan Sakai Ya Yi Wa Wani Mutum Fashi Ya Kuma Halaka Shi A Sokoto

Yadda Ɗan Sakai Ya Yi Wa Wani Mutum Fashi Ya Kuma Halaka Shi A Sokoto

  • Jami'an hukumar NSCDC a Jihar Sokoto sun kama wani tsohon Dan Sakai, Sidiq Kuruwa, kan kashe wani bafulani
  • Kuruwa ya amsa cewa ya bi sahun bafulantanin, Riskuwa Kalamon, a karamar hukumar Tureta, ya masa fashi sannan ya halaka shi
  • Muhammad Dada, Kwamandan Hukumar NSCDC na Jihar, ya ce an kwato shanun da kudi N160,000 daga hannun wanda ake zargi

An kama wani dan haramtaciyyar kungiyar Yan Sakai, Sidiq Kuruwa, saboda fashi da kashe wani bafulatani mai suna Riskuwa Kalamon, a karamar hukumar Tureta a Jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

An gano cewa Kuruwa ta ya sahun bafulatanin ne bayan ya sayar da shanunsa a Kasuwar Tsamiya a yayin da ya ke shirin aurar da yarsa.

Yadda Ɗan Sakai Ya Yi Wa Wani Mutum Fashi Ya Kuma Halaka Shi A Sokoto
Sokoto: Dan Sa Kai Ya Kashe Wani Mutum Bayan Yi Masa Fashi Da Makami. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kuruwa, yayin da jami'an Hukumar Tsaro na NSCDC suka yi holensa ya ce ya raba kudin tare da abokinsa da yanzu ake nemansa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Abin Da Ƴan Boko Haram Suka Faɗa Min A Lokacin Da Muka Haɗu

Ya amsa laifinsa yana mai cewa, "Na siya shanu da kason kudin nawa. Yanzu na yi nadamar abin da na aikata saboda na kashe shi ba tare da wani dalili ba."
Ya kara da cewa abokin aikata laifinsa ya shaida wa yan uwan wanda aka kashe din cewa, "Ni kadai na kashe dan su."

Kwamandan Hukumar NSCDC na Jihar, Muhammad Dada, ya ce an kwato shanun da kudi N160,000 daga hannunsa.

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Kara karanta wannan

Zero Hunger: Sanata Goje ya kaddamar da shirin yakar yunwa a jihar Gombe

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel