Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

  • Yan Jihar Katsina sun yi holen wani mutum dan shekara 22 da ya yi wa wata dattijuwa damfara a Katsina ya ce mata N1.8m
  • Matashin mai suna Aliyu Abdullahi ya samu damar damfarar matan ne bayan ta mika masa katinta na ATM ya taimake ta cire kudi
  • Bayan ya cire mata N10,000 daga ATM, sai ya canja mata katin, ya mika mata nasa bayan ya gano akwai kudi da yawa a nata, ya tafi POS ya cire dukkan kudin ya siya mota da babur

Katsina - Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur
'Dan Shekara 22 a Kstina Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur. Hoto: Vangaurd
Asali: Twitter

Ba wannan bane karonsa na farko

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tambaye shi kan yadda ya fito daga gidan yarin, Aliyu ya ce:

"Lauya na ne ya yi beli na bayan na shafe wata daya a gidan gyaran hali."

Aliyu, wanda a yanzu yana hannun yan sanda, ya amsa cewa ya sauya wa wata Maryam Sale, mai zaune a unguwar Sharar Pipes a Katsina katinta na ATM, ya cire kudin garatutinta da dukkan kudin da ta tara a rayuwanta kimanin Naira miliya daya da dubu dari takwas da dubu arba'in (N1,846,000).

Ya cigaba da cewa:

"Na tafi ATM don cire kudi sai ta zo a Keke Napep ta roke ni in cire mata kudi N10,000 dag asusunta ta hanyar amfani da ATM dina. Kafin in cire mata, na duba kudin da ke ciki sai naga akwai kudi masu yawa. Nan take na cire mata kudin amma na canja katinta da nawa. Bayan ta tafi, na wuce POS na fara cire kudi. Na yi kwana uku kafin na cire dukkan kudin da ke asusun."

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Ya siya mota da babur da kudin

Da aka tambaye shi inda kudin suke, dan damfarar ya ce:

"Na siya mota, Henesy Accord kan N500,000 da kuma sabuwar babur kan N350,000 daga kudin, sauran kuma na yi ta kashe wa wurin siyan kananan abubuwa."

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel