Obasanjo: Abin Da Ƴan Boko Haram Suka Faɗa Min A Lokacin Da Muka Haɗu

Obasanjo: Abin Da Ƴan Boko Haram Suka Faɗa Min A Lokacin Da Muka Haɗu

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bada labarin haduwarsa da yan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram a shekarar 2021, rahoton Daily Trust.

Tsohon shugaban kasar ya gana da wasu yan kungiyar da wasu iyalan Mohammed Yusuf, wanda ya kafa kungiyar.

Obasanjo: Abin Da 'Yan Boko Haram Suka Fada Min Yayin Haduwar Mu
Obasanjo: Abin Da 'Yan Boko Haram Suka Fada Min Lokacin Da Muka Hadu. Hoto: Daily Trust

Da isarsa filin tashi da saukan jirage na Maiduguri, Zanna Umar Mustapha, mataimakin gwamnan Jihar Borno ya tarbi Obasanjo.

Haduwarsu a shekarar 2011

An yi taron ne a tsohuwar hedkwatar kungiyar na tsawon minti 90 tare da yan uwan Yusuf.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke jawabi a wurin taron, Obasanjo ya ce:

"Wannan wani mataki ne da na dauka don kai na. Ina rokon ku ku yi hakuri a yafe abin da ya wuce. Ina rokon ku, ku bani dama in yi sulhu tsakanin ku da gwamnati."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗalibin BUK, Sule, Da Ya Kammala Digiri Da 1st Class

A martaninsa, Babakura Fugu, dan uwan matar Yusuf, wanda aka kashe mahaifinsa a 2009 ya ce:

"Tun shekarar 2009, wannan shine karo na farko da wani babban mutum a kasar nan ya zo ya jajanta ma iyalin mu.
"Muna murna da wannan ziyarar. Kashe 30 zuwa 40 na mambobinmu da suka tafi kasashen Chad, Nijar da Kamaru."

Abin bakin ciki, an bindige Fugu, awa 24 bayan ziyarar Obasanjo.

Kasida ta Gidauniyar Murtala Mohammed

A jawabin da ya yi wurin kasida ta shekara-shekara na Gidauniyar Murtala Mohammed, MMF, wanda aka yi a ranar Litinin, Obasanjo ya ce abin da ya ke tsoro na haduwar Boko Haram da kungiyoyin ta'addanci na kasashen waje ya faru.

Ya ce a lokacin kungiyar ba ta da alaka da yan kasashen waje amma rashin warware matsalar yadda ta dace yasa abin ya zama babban matsala yanzu kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya kuma danganta rashin tsaro a kasar da wanzuwar makamai bayan yakin basasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bayan Ahmed Musa, Wani Ya Sake Yi Wa Tsohon Dan Wasan Super Eagles Kyautar Naira Miliyan 1

Jawabin Obasanjo:

"Babu inda za mu je har sai mun dauki batun tsaron kasa da muhimmanci. Ya zama dole mu gina kasa da kowa ke bada gudunmawa na tsaro. Rashin tsaro ya kunno kai ne saboda wanzuwar makamai kuma tun lokacin ba mu magance matsalar ba, yana kara kazanta.
"A 2011 lokacin da Boko Haram ta fara kunno kai, Na tafi Maiduguri domin in yi bincike kan Boko Haram kuma in san manufansu bayan Sharia, sun koka cewa mambobinsu ba su da aiki kuma a yankurinsu na neman aiki gwamnati na binsu tare da harbe su.
"Abin da na yi tsoro a lokacin shi ke faruwa yanzu. Boko Haram ba ta da alaka da kungiyoyin kasashen waje sosai a lokacin, wadanda suke alaka da su yan Najeriya ne da ke da arziki a kasashen waje ke taimakonsu."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel