Zero Hunger: Sanata Goje ya kaddamar da shirin yakar yunwa a jihar Gombe

Zero Hunger: Sanata Goje ya kaddamar da shirin yakar yunwa a jihar Gombe

  • Sanata daga jihar Gombe ya kaddamar da shirin kawo dauki ga nakasassu a mazabarsa ta Gombe ta tsakiya
  • Sanatan ya ce shirin da ya kirkira ya shirya tallafawa nakasassu akalla 4000 a tsakanin Yamaltu Deba da Akko
  • Hakazalika, a wajen kaddamawar, sanatan ya bayyana manufarsa ta fara tallafawa nakasassu a mazabar tasa

Jihar Gombe - Rahoton da muka samo daga Daily Trust ya nuna cewa sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya kaddamar da shirin rabon kayan abinci ga nakasassu sama da 4,000 a mazabarsa.

Aikin, wanda aka yiwa lakabi da “Zero Hunger”, an shirya shi ne don rage radadin talauci a tsakanin marasa galihu da gajiyayyu a yankin nasa, wanda ya kunshi kananan hukumomin Akko da Yamaltu-Deba.

Goje ya fara rabon kayan abinci
Sanata Goje ya shirya, ya fara gangamin saki da yunwa a jihar Gombe | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Da yake kaddamar da rabon kayayyakin a ranar Lahadi a gidansa da ke Gombe, Sanata Goje, wanda Sakataren shirin, Abubakar Sadiq Kurba, ya wakilta, ya ce sama da mutane 4,390 daga kananan hukumomin biyu ne aka shirya su ci gajiyar shirin.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun hallaka 8, sun sace da dama a Neja

Hon Kurba, wanda dan majalisar dokokin jihar ne, ya bayyana cewa duk wanda ya ci gajiyar shirin zai karbi kunshin da ya kunshi shinkafa, wake, taliyar yara, dabino, man gyada da man ja, kayan yaji, tumatur da turmin zane, kamar yadda Daily Sun ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa an zabi nakasassa su ci gajiyar shirin ne domin kawo musu dauki kasancewar sun fi kowa bukata a cikin al’umma.

Da yake mayar da martani a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Shugaban nakasassu na jihar Gombe, Umar Ali Goro, ya yabawa sanatan bisa wannan karimcin.

Goro ya kuma nemi guraben aikin yi ga nakasassu a jihar tare da kafa wata cibiya ta musamman da za ta ba su sana’o’in hannu.

Kwana 2 a Gamboru: Zulum da Shettima sun raba wa wadanda suka koma gida kudi da kayan abinci

Kara karanta wannan

Neja: An sha yar dirama yayin da kansila ya fatattaki jami’an gwamnati da karnuka da yan daba

A wani labarin, Gwamnan jihar Borno, Frafesa Babagana Umara Zulum tare da Sanata Kashim Shettima sun ziyarci garin Gamboru da ke karamar hukumar Ngala daga ranar Lahadi zuwa Talata.

Shugabannin sun duba tare da shiga cikin masu raba kayan abinci da sauran kayan tallafi ga mutane 60,813 masu gudun hijira da wadanda suka koma yankin.

Zulum da Sanata Shettima sun yi tafiyar ne da motoci kuma a ranar farko ta tafiyar sun bai wa jama'ar yankin Gamboru da Ngala 55,253 kayan abinci da sauran kayan tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel