Buhari ya fi galibin matasar da ke sukansa lafiya, Garba Shehu

Buhari ya fi galibin matasar da ke sukansa lafiya, Garba Shehu

  • Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya ce Buhari ya fi matasan Najeriya da dama da ke caccakarsa lafiya
  • Shehu ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa da manema labarai ta yanar gizo inda yace hotunan Buhari tsuke da kananun kaya sun tabbatar da hakan
  • Mutane sun dinga surutai bayan ganin Buhari ya tsuke da wasu sutturu a kasar Belgium, shigar da ba a saba ganin shugaban kasar yana yi ba

Garba Shehu, kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaba Buhari ya fi matasa da dama da ke caccakar sa lafiya da kwarin jiki, rahoton The Cable.

Shehu ya yi wannan maganar ne ta wata hira da Channels TV a ranar Alhamis wacce aka yi da shi ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Hotunan Shugaba Buhari a tsuke cikin kananan kaya a kasar Belgium sun kayatar

Buhari ya fi galibin matasar da ke sukansa lafiya, Garba Shehu
Mafi yawancin matasan da ke sukan Buhari ba su kai shi lafiya ba, Garba Shehu. Hoto: Fadar Shugaban Najeriya
Asali: Twitter

Yanzu haka Buhari yana Brussels, kasar Belgium don wani taron kungiyoyin hadin kan Turai da Afirka, EU-AU.

Hotunan Buhari tsuke cikin kananun kaya sun tabbatar da lafiyarsa

Wasu hotunan shugaba Buhari ya tsuke da kananun kaya a Belgium, wanda bai saba sanyawa ba sun fara yaduwa a kafafen sada zumunta wanda suka janyo cece-kuce iri-iri.

Yayin da aka bukaci tsokacin Shehu akan shigar cewa ya yi ‘yan Najeriya sun fara yarda da cewa shugaban kasa yana cikin koshin lafiya bayan ganin hotunan nashi.

Kamar yadda ya shaida:

“Shugaban kasa yana da lafiya. Yanzu mutane da dama sun fara yarda da cewa yana cikin koshin lafiya bayan ganin hotunan sa da kananun kaya.
“Ya kamata hotunan su gusar da fargabar da mutane suke yi. Ana ta yada labaran karya akan lafiyar Buhari inda mutane suke ta tunani mara kyau. Mutane basu san komai ba.”

Kara karanta wannan

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

Daga hawan Buhari mulki kawo yanzu, ya kwashe kwana 170 a Ingila don ziyarar ganin likita

Ya kara da cewa:

“Mun dade muna cewa Buhari ya fi matasa da dama lafiya, musamman masu caccakar sa. Shigar da ya yi a Belgium na nuna cewa gaskiya ce maganar nan.”

Tun bayan shugaban kasa ya hau karagar mulki, ya dinga kai ziyara Ingila don a duba lafiyarsa, lamarin da ya yi ta janyo cece-kuce.

A 2021, The Cable ta ruwaito yadda shugaban kasa ya kai ziyara Ingila don a duba laifiyar sa inda ya kwashe fiye da kwana 170 tun daga hawar sa mulki.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel