Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya ji dadin yadda masu hannu da shunin Najeriya suka fahimci cewa aikin kowa ne gyara Najeriya
  • Buhari ya yi wannan furucin ne a wata liyafar kwamitin shugabannin kasuwanci, siyasa, kafafen yada labarai da ma’aikata na 2022 da aka yi ranar Lahadi
  • Dama a watan Janairun 2021 ne shugaba Buhari ya zargin kusoshin Najeriya da kai wa mulkin sa cikas duk da kokarin da yake yi wa kasa

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane
Buhari: Na Yi Murnar Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Akwai lokacin da ya bukaci kusoshin Najeriya da su yi adalci wurin caccakar gwamnatin sa, inda ya ce ba sa yaba wa mulkin sa duk da kokarin da yake yi.

Buhari ya taba zargin kusoshin kasar nan da hada kai da ma’aikatan kasashen waje wurin tatsar kasar

Ya taba zargin su da bijiro da bukatu masu tsada da kuma hada kai da ma’aikatun kasashen waje don damfarar kasar su.

Shugaban kasa ya kula da yadda suke caccakar sa inda yace da kusoshi suna taimaka masa da sai ya fi haka samun nasarori.

Kara karanta wannan

Magaji na zai riski daidaitacciyar damokaradiyya da ingantaccen tsarin tsaro, Buhari

A cewar Buhari:

“Na shirya wannan taron ne don in gane manufar ku ta hada kai da gwamnati na ta ko ina.
“Ya kamata ‘yan siyasan cikin ku su nemi hanyar kawo gyara a kasa banda samun mukamai. Ga ‘yan kasuwa maza da mata kuwa akwai alheri wurin yi wa jama’a aiki.
“Ina jin dadin ganin cewa kusoshin Najeriya sun fahimci cewa aikin kowa ne sauya kasar mu don ba aikin gwamnati kadai bane.”

Buhari ya ce ya kamata a hada kai wurin bunkasa Najeriya

Ya kara da cewa babu yadda za ayi mutum ya zauna yana tunanin abinda ya wuce don haka mu ne ya dace mu kawo wa Najeriya mafita matukar muna son alfahari da ita.

Ya ce kowa ya san idan shugabannin ‘yan siyasa, na addini da na al’ada suka hada kai don yin aiki tare saboda ci gaban kasa, hakan zai samar da ingantacciyar kasa.

Akwai kusoshin da idan suka zage wurin samar da riba za su kawo ci gaba ga wasu masana’antun na daban.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ministan Buhari ya bayyana matsayinsa kan tsayawa takarar kujerar

Ya ce ya ji dadin yadda yanzu masana’antu suka fara ganin kawo hanyoyin kawo karshen matsalolin kasar nan.

2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara

A wani rahoton, fiye da malaman addinai na Kirista da musulunci sun taru a Abuja ranar Juma’a suna nuna goyon baya ga gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello don ya zama shugaban kasa a 2023, The Nation ta ruwaito.

Malaman sun ce Bello ne ya dace da ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023 sakamakon ayyukan da suka gani ya yi a Jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel