Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

  • Hukumar yaki da fatauncin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta sanar da yadda Abba Kyari suka yi harka da dillalin kwayoyi daga Brazil
  • Kamar yadda Aba Kyari ya bayyana, sun yi magana da dillalin kan miyagun kwayoyin suna tafe, kuma jami'ansu sun tsaya a filin jirgin domin amsa
  • NDLEA ta ce babu hannun jami'anta a cikin harkar, 'yan sanda ne suke tsayawa a ciki da wajene filin sauka da tashin jiragen saman domin harkarsu

Hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce, babu ruwan ma'aikatan ta da sabgar hodar iblis mai nauyin kilogram 25 da ya hada da tawagar yan sanda karkashin jagoranci mataimakin kwamishinan 'yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari.

A wata takarda da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Laraba, ya dora laifin a kan ma'aikatan hukumar 'yan sanda da kuma yadda wadanda ake zargin suka shirin shigo da haramtattun ababen daga Addis Ababa, Ethiopia.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da shahararren dillalin kwayoyi a Brazil, NDLEA
Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da shahararren dillalin kwayoyi a Brazil, NDLEA. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

'Yan sanda ne ke ikirari a wata takarda da suka fita ranar Litinin cewa, ma'aikatan NDLEA suna da sa hannu a harkallar.

Sai dai, ba tare da nuna martani ga maganar 'yan sandan ba Mr Babafemi ya nuna rashin amincewa da ikirarin, wanda ya siffanta da tuntuben harshe.

Sabani dangane da ikirarin, Mr Babafemi ya ce, a iya binciken da a ka yi ya, nuna cewa Abba Kyari da tawagar shi ta 'yan sanda ne wadanda suka yi safarar hodar iblis din kuma su ne kai tsaye suke harka da dillalin kwayoyin daga kasar Brazil.

A cewar NDLEA:

"Tabbatattun shaidu sun bayyana yadda masu safarar miyagun kwayoyin suka tuntubi tawagar Abba Kyari, kuma ba tare da tamtama ba alamu sun nuna karara yadda kungiyar tasu ke aiki."

Kara karanta wannan

Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa

Yadda tawagar Abba Kyari suka tsara da masu safarar miyagun kwayoyi

"Idan an tuna, bayan NDLEA ta bukaci kama Abba Kyari da wasu mutum hudu, 'yan sandan sun tuhume su, inda daga baya suka mika su tare da rahoton kama sun," a cewar Babafemi yayin bayyana yadda Kyari ya jagoranci tawagar a harkallar miyagun kwayoyin.

Kamar yadda takardar da NDLEA ta saki, ta nuna bayanan yadda Kyarin yayi ciniki da wanda ya kawo mishi bayanin a kan yadda za su kasafta ribar da aka samu na laifin da ake zargin su dashi.

"Yayin bada amsa ga tambayar ma'aikacinmu a kan ko yaran shi suna tsayawa ciki ko wajen filin jirgi, Abba Kyarin ya ce, 'Eh, eh, wasu na tsayawa waje, wasu kuma ciki. Kawai barin mu suke mu gama dabarbarun isowa.

"Wannan maganar ba shakka ta tabbatar da yadda masu safarar miyagun abubuwan suke ta'ammuli da masu alhakin kama su. Kuma, wannan dan gyara kurakurai ne a wasu rahotannin da kuma bayar da tabbacin cewa, hukumar ba za ta kauce daga wani shaidar binciken ba, sannan ba za ta raga wa duk wanda ke da alhaki ba," yace

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Takardar NDLEA ta zo ne a matsayin fashin baki ga hukumar 'yan sanda, wacce a ranar Litinin, ta nuna yadda ma'aikatan hukumar ke sabgar hodar iblis.

Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa

A wani labari na daban, sabon labari ya bayyana a kan yadda sifeta janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba da shugaban hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), Birgediya janar Buba Marwa, suka hadu a hedkwatocin tsaro dake Abuja.

Sun yanke shawarar yadda za su bullo wa lamarin kwamandan hukumar binciken sirri na 'yan sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyari, bisa hannunsa a harkallar safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 25.

Bayanin yazo ne bayan kwana daya da 'yan sanda suka dakatar da duk wasu rassa na IRT na jihohin dake fadin kasar, wanda hakan ya biyo bayan kama DCP Kyari da aka yi.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel