Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

  • Mutuwar mazaje a dakunan Otal yayinda suka kai mata shakatawa ya fara zama ruwan dare a Najeriya
  • Kusan duka wadanda wannan ibtila'i ya fadawa kwanakin nan basu rasa alaka da shan maganin kafin maza ba
  • Hukumomin lafiya sun gargadi maza kan shan kwayoyin dake kara karfi azzakari

Jihar Rivers - Wani mutumi yayi numfashinsa ta karshe a dakin Otal dake Ada George, karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers bayan shakatawa da yarinya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne yan awanni bayan shigarsu cikin daki da yarinyar ranar Laraba.

Police
Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

Wani mutumi da ya ziyarci Otal din kuma ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa misalin karfe 2 na dare, yarinyar ta fito daga cikin dakin tana iwu tana neman dauki saboda mutumin da take tare da shi ya yanke jiki ya fadi.

Kara karanta wannan

Adashin N2,000 take kullum: Jami'ai kan mabaraciyar da aka kama da N500,000 da $100 a Abuja

A cewarsa, manajan Otal da masu gadi suka dira wajen kuma suka garzaya da shi asibiti.

An tattaro cewa an isa asibitin mutumin yace ga garinku.

Wani mai idon shaida wanda ya bukace a boye sunansa yace yarinyar ta bayyana yadda mutumin ya sha maganin karfin maza kafin suka shiga daki.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Grace Iringe-Kokom, ta tabbatar da labarin inda tace tuni an damke manajan Otal da yarinyar.

A cewarta:

"Lallai muna sane da abinda ya faru a Otal din kuma ana gudanar da bincike. Jami'anmu sun damke matar da Manajan Otal."

Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja

Haka kwanakin baya wani mutumi ya mutu a unguwar Kubwa dake karamar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja yayinda ya kai yarinya dalin Otal don shakatawa.

An tattaro cewa wannan abu ya faru ne da daren Litinin.

Mutumin mai suna, Ogunleye Emmanuel, ya shiga da yarinya dakin ne amma bai fito ba.

Kara karanta wannan

Ahmad Musa ya yiwa tsohon dan kwallon da ya talauce kyautar N2m

Wani mai gidan Otal a unguwar wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace:

"Mutumin ya yanke jiki ya fadi yayinda yake tare da yarinyar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel