Hotunan Shugaba Buhari a tsuke cikin kananan kaya a kasar Belgium sun kayatar

Hotunan Shugaba Buhari a tsuke cikin kananan kaya a kasar Belgium sun kayatar

  • Hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari tsuke da kananan kaya a birnin Brussels da ke Belgium sun yadu a kafafen sada zumunta
  • Tun bayan wallafa hotunan da hadiminsa Bashir Ahmad yayi inda yake tare da Shugaba Umaro Sissoco na Guinea-Bissau, jama'a ke ta tsokaci
  • Hakan ba ya rasa alaka da sabon ganin shugaban kasan da aka yi da manyan kaya ko da kuwa cikin Turawa zai shiga a kasashen ketare

Brussels, Belgium - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a wasu hotuna sanye da kananan kaya inda ya tsuke.

Kyawawan hotunan sun dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani tun daga ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairu yayin da ya ke ganawa da shugaban kasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo yayin taron kungiyoyin gamayyar Turai da Afrika a birnin Brussels da ke Belgium.

Kara karanta wannan

Buhari ya fi galibin matasar da ke sukansa lafiya, Garba Shehu

Hotunan Shugaba Buhari a tsuke cikin kananan kaya a kasar Belgium sun kayatar
Hotunan Shugaba Buhari a tsuke cikin kananan kaya a kasar Belgium sun kayatar. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Bayan wallafa hotunn shugaban kasan da hadiminsa Bashir Ahmad yayi a shafinsa na Twitter, jama'a sun dinga yada hotunan ganin kananan kaya ne a jikin shugaban kasa.

A lokuta da yawa an fi ganin shugaba Buhari sanye da manyan kaya ko da kuwa kasashen ketare ya je cikin Turawa.

Shugaba Buhari zai shilla kasar Belgium halartar wani taro

Legit.ng ta ruwaito cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a yau dinnan zuwa kasar Belgium domin halartar wani taron shugabannin duniya.

Sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga mai taimakawa Buhari a harkokin yada labarai ta ce, shugaban zai dawo Najeriya ranar Asabar idan Allah ya kaimu.

Sanarwar ta karanta cewa:

"A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja domin halartar taron shugabannin kasashen Turai da na Afirka da kuma shugabannin kungiyoyi da dama a taron kungiyar Tarayyar Turai da kasashen Afirka (EU-AU) karo na 6 a birnin Brussels na kasar Belgium. Ana sa ran shugaban zai dawo kasar ranar Asabar."

Kara karanta wannan

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

Asali: Legit.ng

Online view pixel