Buhari ya gaza: PDP ta nemi Buhari ya sauka daga kujerar ministan mai, ta fadi dalili

Buhari ya gaza: PDP ta nemi Buhari ya sauka daga kujerar ministan mai, ta fadi dalili

  • An bukaci karamin ministan man fetur Timpre Sylva da ya yi murabus daga mukaminsa saboda shigo da gurbataccen man fetur da aka yi Najeriya
  • Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP ne ya yi wannan kiran a ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairu a martaninsa na cece-kuce kan man fetur a kwanan nan
  • A cewar jam’iyyar PDP, gwamnatin da APC ke jagoranta na neman hanyoyin da za a bi ta tara kudade ne kawai domin biyan bukatun jam’iyyar gabanin zabe mai zuwa

Biyo bayan kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta tun bayan rahotannin shigo da gurbataccen man fetur cikin kasar, jam’iyyar PDP ta bukaci karamin ministan mai, Timipre Sylva ya yi murabus.

Hakzalika, jam'iyyar ta nemi shugaba Buhari ya sauka daga mukamin babban ministan ma'aikatar albarkatun man fetur ya mika wa kwararru su rike kujerar, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya sanyawa hannu, ta yi gargadin cewa jagorancin jam’iyya mai ci ta APC ne ke tursasa ‘yan Najeriya su fito kan tituna suna zanga-zanga.

Jam'iyyar PDP ta yi kira ga Buhari
Buhari ya gaza: PDP ta nemi Buhari ya sauka a matsayin ministan man fetur, ta fadi dalili | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A sanarwar da TheCable tace ta gani, ta ce zanga-zangar nuna adawa da gwamnati mai ci na tasowa ne saboda ci gaba da ganin cin hanci da rashawa da rashin kula da jin dadin jama'a da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi.

Ologunagba ya kuma gargadi jam’iyyar APC akan zargin boye shugabannin jam’iyyar na shigo da gurbataccen man fetur cikin kasar.

Zargin wawure dukiyar al'umma

A bangaren PDP, wannan yunkuri na gwamnati mai ci ya nuna sha’awar APC na yin wasoson kudi daga asusun kasa.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Jam’iyyar ta yi zargin matakin da ministan ya dauka na neman Naira biliyan 201 saboda tsaftace gurbataccen man maimakon fallasa masu laifin da kuma gurfanar dasu.

Ologunagba ya kara da cewa, jam’iyya mai mulki na yin kunnen uwar shegu da kukan da ‘yan Najeriya ke yi na kawo karshen matsalar cin hanci da rashawa da ake tafkawa a baitul malin kasar.

A kalamansa:

"Don haka jam’iyyar PDP ta yi kira da a gaggauta sallamar karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva saboda yaudarar ‘yan Najeriya da boye wasu muhimman bayanai."

Hakazalika, PDP ta nemi Buhari ya mika wa wani wanda ya dace ya rike kujerarsa ta ministan albarkatun man fetur tunda ya gaza.

A cewa PDP:

"Jam'iyyar PDP ta kuma bukaci shugaba Buhari tun da ya gaza, ya sauke nauyin da ya ratayawa kansa na matsayin ministan albarkatun man fetur tare da baiwa kwararru damar rike ma'aikatar domin ta dawo hayyacinta."

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku sake damƙa amanar Najeriya hannun APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Tsadar mai: Bidiyo ya fallasa yadda ake sayar da gurbataccen mai a wani gidan mai

A wani labarin, yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ta kowane bangare, wasu masu gidajen mai suna kara wa ciwon gishiri ta hanyar sayar da gurbataccen mai.

Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya bayyana lokacin da wani ma'aikacin gidan mai ke kokarin cika wata gorar ruwa da wani mai launin ja da ya yi kama da gurbatacce.

A bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo a kan shafin Facebook na jaridar Punch, an ga man da ake dura wa gorar da launin da bai yi kama da na man fetur ko kalanzir ko gas ba, duk da cewa a gidan mai ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel