Ku taimaka ku cigaba da amincewa da jam'iyyar APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Ku taimaka ku cigaba da amincewa da jam'iyyar APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya yi ikirarin cewa APC ta bai wa mara ɗa kunya duk da karancin kuɗin shiga
  • Sanatan ya kuma roki yan Najeriya su cigaba da mara wa APC baya a 2023, domin ta shawo kan matsalolin da PDP ta gina a baya
  • A cewarsa. gwamnatin APC ta aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa fiye da wanda PDP ta yi a shekara 16

Lagos - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawal, ya roki yan Najeriya su cigaba da miƙa kula da amanar Najeriya hannun jam'iyyar APC domin jam'iyya ce mai gaskiya.

Lawan ya yi wannan rokon ne ranar Lahadi a Legas, a wurin taron samarwa mutane jari karo na 5, na sanata mai wakiltar Legas ta yamma, Solomon Olamilekan.

Leadership ta rahoto cewa taron wanda ya gudana a harabar makarantar yan sanda dake Ikeja, ya samu halartar gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Ahma Ibrahim Lawan
Ku taimaka ku cigaba da amincewa da jam'iyyar APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

A wata sanarwa da kakakin shugaban majalisar dattawa, Ola Awoniyi, ya fitar, Sanata Lawan, ya bayyana jihar Legas a matsayin gidan APC.

Sanatan ya kuma jaddada kwarin guiwarsa da cewa:

"Da izinin Allah, jam'iyyar APC ce zata cigaba da mulkin jihar Legas da kuma Najeriya. Abin da muke bukata shi ne mu cigaba da ayyukan alherin da muka saba."
"PDP ka iya faɗa muku abun dariya game da gwamnatin APC a matakin ƙasa, amma kusani ta jagorancin Najeriya na shekaru 16, basu yi komai ba sai barin tulin matsaloli gare mu a 2015."
"Muna kokarin shawo kan waɗan nan matsaloli, zata yuwu wajen kokarin magance matsala wata kuma ta kunno kai, muna iya bakin kokari."

A kwana a tashi zamu cimma gaci - Lawan

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Lawan ya ƙara da cewa da yardar Allah APC zata gyara Najeriya duk da kalubalen da ake fuskanta ta bangaren tsaro.

"Idan wani ya faɗa maka ba abin da APC ta iya sai ciyo bashi, ita PDP ta kwashe shekara 16 ga makudan kuɗin shiga amma babu wani ayyuka raya ƙasa da ta yi da yawa idan ma akwai."
"Ba mu ƙaunar ciyo bashin nan, amma idan ba mu da wani zaɓi, ga manyan ayyukan da zasu kawo cigaba a ƙasa, shin me kuke tunanin zamu yi?"

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya watsa wa gwamnonin APC biyu ƙasa a ido, ya ƙi amincewa da bukatarsu

Shugaba Buhari ya watsa wa wasu gwamnonin APC biyu ƙasa a Ido, ya umarci su bi matakai matukar suna son ya amince.

Rahoto ya nuna cewa gwamnonin sun garzaya ga Buhari ne domin ya goyi bayan ɗan takarar da suke so ya zama shugaban APC.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Asali: Legit.ng

Online view pixel