Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina

Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina

  • Wani matashi mai shekaru 16, Abubakar Abdulbasir, ya shiga hannu bisa zargin garkuwa da wata yar'uwarsa
  • Bayan sace yarinyar da ya yi, sai matashin ya kira iyayenta sannan ya nemi su biya N70,000 kudin fansa ko kuma su rasa ta
  • Kakakin yan sandan jihar, Isah Gambo ya tabbatar da lamarin ga manema labarai

Wata mata da ke wucewa ta wani kango a garin Marabar Kankara da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina ta ceto yarinya yar shekara hudu da aka yi garkuwa da ita, lamarin da ya taimaka wajen kama wanda ya sace ta.

A bisa ga rahoton yan sanda, matar wacce ke sane da batun batar yarinyar mai shekaru hudu, tana wucewa ta wani kango a yankin, sai ta hango yarinyar tare da wani Abubakar Abdulbasir.

Kara karanta wannan

Ango ya barke da kuka wajen bikin aurensu saboda tuna mutuncin da Amarya tayi masa

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wanda ake zargin, Abubakar Abdulbasir mai shekaru 16 yana a aji uku na karamar sakandare ne a garin.

Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina
Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Majiyoyi sun kawo cewa lokacin da matar ta tambayi Abdulbasir kan abun da yake yi da karamar yarinyar, sai ya ce suna dai hira ne amma ya ce mata tana iya tafiya da ita gida, ita kuma sai ta aikata hakan.

Da ta kai yarinyar gida sannan ta sanar da haduwarsu ga iyayenta, sai mahaifin ya kai kara ofishin yan sandan Malumfashi sannan aka gayyaci mahaifin Andulbasir don amsa tambayoyi game da inda dansa ya shiga, wanda ya tsere a lokacin.

Bayan Abdulbasir ya dawo gida, sai mahaifiyarsa ta fada masa cewa yan sanda sun gayyaci mahaifinsa sannan an tambaye shi game da inda ya shiga. Hakan ya sa shi tafiya ofishin yan sanda sannan ya tona asirin cewa ya aikata laifin.

Kara karanta wannan

Ango ya bindige amarya, mutum 3 da kan shi yayin zaman sulhun gyara aurensu

Matashin ya ce:

“Eh da gaske ne cewa na yi garkuwa da yar’uwata Halima. Na boye ta a wani kango a wajen gari sannan na kira iyayenta na nemi su biya N70,000. Na kuma yi barazanar cewa idan suka ki kawo kudin suna iya rasa ta. Nan take, sai na kashe wayan, zuciyata ta fada mani cewa hanyar da na dauka ba mai bullewa bace kuma addinina ya hani da hakan.
“Ayi hakuri da abun da nayi. Ina neman afuwa. Na gane kuskurena.”

Da yake jawabi ga manema labarai a yayin gurfanar da mai laifin, kakakin yan sandan jihar, SP Isah Gambo ya ce:

“Wani Sanusi Abubakar na kauyen Marabar-Kankara a karamar hukumar Malumfashi ya kai kara ofishin yan sanda cewa yarsa mai shekaru 4, Halimatu Sanusi ta bata kuma duk kokarin da aka yi na gano inda take ya ci tura. Daga bisani sai ya amsa kiran waya cewa anyi garkuwa da yarsa, kuma aka yi masa barazanar cewa ya biya N70,000 ko ya rasa ta.

Kara karanta wannan

Wani Saurayi ya lakadawa budurwarsa duka har ta mutu bayan ya dirka mata ciki

“Nan take sai yan sanda suka shiga aiki, inda suka gudanar da bincike wanda ya kai ga kama wanda ya kitsa abun, wani Abubakar Abdulbasir mai shekaru 16 na kauyen Marabar-Kankara. A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.”

Rashin tsaro: Gwamnatin Katsina ta haramta kungiyar Yan-Sa-Kai a fadin jihar

A gefe guda, gwamnatin jihar Katsina a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, ta sanar da haramta kungiyar Yan-sa-kai a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki matakin ne saboda yawan laifukan da mambobin kungiyar ke aikatawa.

Kungiyar na dauke ne da mutanen da suka sadaukar da kansu domin taimakawa a lamuran tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel