Ango ya bindige amarya, mutum 3 da kan shi yayin zaman sulhun gyara aurensu

Ango ya bindige amarya, mutum 3 da kan shi yayin zaman sulhun gyara aurensu

  • Wani ango dan kasar Misira ya bindige matarsa, yan uwan shi uku da kanshi yayin zaman sasanci tsakanin aurensa da amaryarsa
  • An samu labarin yadda matashin mai sana'ar kyadi, dan shekara 22 ya fusata matuka, wanda hakan yasa ya aikasu barzahu
  • Sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da yadda aka taba kwantar da mutumin a asibitin mahaukata watanni bakwai da suka wuce

Wani magidanci dan kasar Misira ya bindige matarsa, mutane uku a dangin shi da kan shi yayin zaman sasancin aure a birnin Cairo, makwanni kadan bayan auren nasu.

Al Jazeera sashin larabci ta bada labarin yadda a daren Juma'a, wani mutum dan shekara 22 mai suna Shams Shariff, ya boye bindiga a jaka, inda ya tafi da ita zama tsakanin iyalan biyu a kusa da babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Magidanci ya bindige matarsa, mutum 3 da kan shi yayin zaman sulhun gyara aurensu
Magidanci ya bindige matarsa, mutum 3 da kan shi yayin zaman sulhun gyara aurensu. Hoto daga thenationonlinegn.net
Asali: UGC

A lokacin da ana tsaka da zaman, iyalan sun yi kokarin ganin sun sulhunta rikicin, wanda hakan ne ya fusata sa, ya bindige amaryarsa mai suna Nour Ghazal mai shekaru 20 da mahaifiyar ta, mai shekaru 58 mai suna Mona Mohamed.

Kananan jaridu sun ruwaito yadda Shams ya fara harbe yar uwar tasa, Sherine mai shekaru 42 da mijin ta Khaled Mohamed mai Shekaru 53,sannan ya kashe kan shi.

Makwabta sun jiyo karar harbe-harben, hakan yasa suka shaidawa 'yan sanda. Babu wanda ya rayu cikin mutane biyar din, The Nation ta ruwaito.

An samu labarin yadda aka taba kwantar da mijin, wanda ke sana'ar kyadi, a asibitin mahauka a watanni bakwai da suka wuce.

Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu saɓani a Nasarawa

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

A wani labari na daban, Mutanen unguwar Sabon Pegi-Shubu, a karamar hukumar Lafia ta Arewa, Jihar Nasarawa, a ranar Juma'a sun shiga jimami da alhini bayan wani magidanci ya yi matarsa mai 'ya'ya uku duka har ta mutu bayan sabani ya shiga tsakaninsu, rahoton Vanguard.

An gano cewa rikicin ya samo asali ne a lokacin da matar auren, marigayiya Esther Aya ta kira wani kafinta domin ya gyara tagar gidan saboda sauro su dena shiga, da mijin ya dawo sai ya umurci kafintan ya dena aikin, hakan ya fusata matar.

Vanguard ta rahoto cewa wani da ya yi magana amma ya nemi a boye sunansa, kuma ya yi ikirarin shine kafintan ya ce mijin marigayiya Esther ya fatattake shi yayin da ya ke kokarin gyara ragar da ke tagar gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel