Bayan ɗirka mata ciki ta haifi jariri, Saurayi ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta koma ga Allah

Bayan ɗirka mata ciki ta haifi jariri, Saurayi ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta koma ga Allah

  • Ana zargin wani saurayi da kashe budurwarsa da suke rayuwa tare bayan ya mata ciki kuma ta haifa masa yaro a Anambra
  • Wata shaidar gani da ido ta tabbatar da cewa Saurayin ya lakada wa matar duka, ta yanke jiki ta faɗi, kuma ta karisa mutuwa a Asibiti
  • Lamarin ya fusata matasan yankin waɗan da suka yi doka kan haka, saura kiris su kashe shi yan Bijilanti suka kwace shi

Anambra - Wani Saurayi ya kashe budurwarsa yar kimanin shekara 22 a duniya a yankin Mgbakwu, ƙaramar hukumar Awka North, jihar Anambra.

Wata shaidar gani da ido, Ngozi Nwude, tace wanda ake zargin, Ikenna Oraekie, ya maida dukan yarinyar tamkar ɗabi'arsa duk da gargaɗin da makotansa suka masa.

Tace masoyan biyu sun jima suna tare, watanni shida kenan da haihuwarta duk da ba'a biya sadaki ba, amma ya mata ciki, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

Kara karanta wannan

An kama wata mata a Kano tana yunƙurin sace yaro ɗan shekara 5 a hanyarsa ta zuwa makaranta

Taswirar Jahar Anambra
Bayan ɗirka mata ciki ta haifi jariri, Saurayi ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta koma ga Allah Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shaidar tace:

"Tuntuni take tare da matashin saurayin, yar asalin garin Enugwu Agidi, ƙaramar hukumar Njikoka, amma mahaifiyarta yar nan Mgbakwu ce."
"Ikenna Oraekie ya lakaɗa mata duka daga bisani ta yanke jiki ta faɗi, nan take aka kaita Asibiti, likita ya tabbatar masa da cewa ta mutu."
"Wasu matasa da suka san abin da ya auku, bayan ganin gawarta, nan da nan suka hau kan shi da duka, suka masa jina-jina. Sun yi kokarin ƙona shi, amma yan Bijilanti suka iso, suka kwace shi zuwa ofishin su."

Wane hali ake ciki yanzu haka?

Rahoton da muka tattara ya nuna cewa har yanzun gawar matashiyar budurwan na can kwance a ɗakinta, yayin da matasa suka mamaye ofishin yan Bijilanti suna bukatar a basu shi su kashe shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagu sun kashe mataimakin kwamishinan yan sanda

Wani bincike ya tabbatar da cewa mutanen dake zaune a yankin sun amince duk wanda ya kashe wani, shi ma zasu kashe shi kuna su ƙona gidansa.

Wannan ya biyo bayan wani lamari mai kama da wannan da ya auku, wani mutumi ya kashe mace, mutane suka kashe shi kuma suka ƙona gidansa a yankin.

A wani labarin na daban kuma Mahaifi ya ɗirka wa diyarsa ta jini ciki saboda tsabar sha'awa

Yan sanda sun yi ram da wani mahaifi dan kimanin shekara 38 bisa zargin ɗirka wa ɗiyarsa ta jini juna biyu a jihar Bayelsa.

Makotan mutumin sun bayyana cewa lamarin ya soma ne bayan mutuwar mahaifiyar yarinyar, inda ya maye gurbinta ta ɗiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel