Ango ya barke da kuka wajen bikin aurensu saboda tuna mutuncin da Amarya tayi masa

Ango ya barke da kuka wajen bikin aurensu saboda tuna mutuncin da Amarya tayi masa

  • Wani mutumin Najeriya, Mista Majekodunmi Abayomi, ya fashe da kuka ana bikin aurensa
  • Abin da ya sa Majekodunmi Abayomi kuka shi ne tunawa da irin alherin da matar tayi masa
  • A cewar Angon, a dalilin matarsa ne ya samu zuwa kasar waje bayan ta je yin karatun digirgir

An samu wani mutumi da labarinsa ya karada shafukan sada zumunta na zamani saboda yadda ya rika kika a wajen bikin aurensa.

A wasu sakonni da ya fitar a shafinsa na Twitter kwanaki, Majekodunmi Abayomi ya bada labarin yadda matarsa ta taimaka masa.

Abayomi ya ce ya hadu da wannan mutumiyar kirki da ta zama matarsa ne a shekarar 2018.

Kamar yadda Majekodunmi Abayomi ya fada, sa’ilin da ya fara haduwa da amaryar a, albashinta ya ribanya na sa kusan sau daya da rabi.

Kara karanta wannan

Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari

Angon ya ce duk da cewa budurwarsa ta na karbar albashi mai tsokan da ya zarce na sa, hakan bai kawo wata tangarda a soyayyarta su.

Ta samu zuwa kasar waje

A shekarar 2020 amaryar ta samu damar zuwa Turai domin yin digirgir, daga nan ta fara ba Abayomi shawarar su tattara, su koma ketare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da bai da niyyar barin Najeriya, sai Mista Abayomi ya shiga neman damar zuwa karo karatu a jami’o’in kasashen waje tare da masoyiyarsa.

Majekodunmi Abayomi
Majekodunmi Abayomi da Debby Brown Hoto:@Hardey_dayor Daga: Twitter
Asali: Twitter
“Ta bani kwarin gwiwar neman digirgir a waje, na ku ma yi dace, na yi ta samun damar karatu ba tare da an dauke mani kudin makaranta ba.”

- @Hardey_dayor.

Neman biza

Lauyan ya ce sai ya roki budurwar su yi aure kurum, ya kuma yi niyyar neman takardar biza domin ya hadu da sahibarsa a Turai.

Kara karanta wannan

Duk a cikin so ne: Saurayi ya kaftawa budurwarsa mari sannan ya roki ta aureshi

Ba tare da ya sani ba, ashe wannan matar ta zagaya ta nemi alfarama a ba ta damar zuwa kasar waje da mijinta saboda gudun kadaici.

Aka yi dace, aka karbi shawarar da ta kawo, sai ga shi wadannan Bayin Allah sun bar Najeriya tare, ita ce ta buda masa hanyar alheri.

Abayomi a shafinsa na Twitter ya yabi matarsa @IAmDebbyBrown, ya ce saboda ita ya zo Turai. Wannan ya sa shi kuka a wajen bikinsu.

“Yau ina Turai ne saboda kirkin matata @IAmDebbyBrown, bayan yarda da ni da tayi, ta kaunace ni, tayi mani duk abin da za ta iya.”
“Ta yi bakin gwargwadonta, nan na san kokarin mace idan har ta na neman wani abin.” - @Hardey_dayor.

Asali: Legit.ng

Online view pixel