Tashin hankali: Bidiyon yadda dan sanda ya boye yayin da 'yan bindiga suka kai hari

Tashin hankali: Bidiyon yadda dan sanda ya boye yayin da 'yan bindiga suka kai hari

  • A ranar Alhamis 10 ga watan Fabrairu ne aka kai wa wani shingen bincike na ‘yan sanda hari a jihar Enugu inda aka ce an kashe ‘yan sanda uku
  • ‘Yan bindigar sun kuma kai hari a shingen binciken jami’an kwastam da ke kusa da asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya da ke jihar
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da faruwar hare-haren tare da tabbatar wa mazauna garin cewa ana ci gaba da kokarin cafke wadanda suka kai harin

Jihar Enugu - Wasu ‘yan bindiga a ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu, sun harbe ‘yan sanda a wani shingen bincike da ke kusa da Estate Ulumalinda a karamar hukumar Enugu ta Kudu a jihar ta Enugu.

An ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wata mata a kan titin bayan farmakin da shaidun gani da ido suka ce an kwashe kusan mintuna 30 ana yi ba tare da samun mai kalubalantarsu ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun farmaki kauye saboda kai kararsu ga jami'an tsaro

Enugu ta shaida mummunan harin 'yan bindiga
Tashin hankali: Dan sanda ya buya a shago yayin da 'yan bindiga suka farmake su | Hoto: commons.wikimedia.org
Asali: UGC

Wani ganau ya shaida wa jaridar Punch cewa ‘yan bindigar sun yi wa wata mai shagon hada-hadar kudi na POS fashi bayan wani harsashi da ya same ta.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘yan bindigar sun kuma kai hari a shingen binciken kwastam da ke cikin unguwar Ozalla da ke kan titin Enugu zuwa Fatakwal, kusa da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wani shaidar gani da ido, ‘yan bindigar sun bude wuta kan jami’an Kwastam, inda nan take mutum daya ya mutu tare da jikkata wasu uku.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wani ma’aikacin napep ya samu rauni a yayin da ‘yan bindigar ke harbin iska don tsoratar da mutane.

Bidiyon dan sandan da ya firgita, ya buya yayin harin Enugu da aka yada a shafin Twitter

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Mai jego, jariri da wasu mutane a Kaduna a daren Juma'a

A bangare guda, wani faifan bidiyo na wani dan sandan da ya tsira da ransa ya bayyana a shafin Twitter.

TweetieTosin ne ya yada bidiyon a shafin Twitter, inda ya bayyana yadda lamarin ya faru tare da koka yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa.

Kalli bidiyon:

Yan sanda sun yi kazamar musayar wuta da yan bindiga a Katsina, sun halaka da dama

A wani labarin, Gwarazan yan sanda sun samu nasarar daƙile wani kazamin harin yan bindiga da suka addabi jihar, sun sheke guda 5 sun kwato mutanen da aka sace da dabbobi.

Vanguard ta rahoto cewa yan bindigan sun yi yunkurin kai hari kauyukan Kuru da Dangani a karamar hukumar Musawa jihar Katsina.

Sauran abubuwan da yan sandan suka kwato sun haɗa da, bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da zaren alburusai da kuma Mota kirar Gulf III.

Asali: Legit.ng

Online view pixel