Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun yi kazamar musayar wuta da yan bindiga a Katsina, sun halaka da dama

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun yi kazamar musayar wuta da yan bindiga a Katsina, sun halaka da dama

  • Gwarazan yan sanda a jihar Katsina sun yi artabu da yan ta'adda yayin da suka kai hari kauyukan karamar hukumar Musawa
  • SP Gambo Isa, Kakakin yan sanda na jihar, yace kwamandan yan sanda na yankin Dutsinma ya jagoranci tawagarsa suka dakile harin
  • Yace yan sanda sun kashe yan ta'adda biyar, sun ceto wani mutumi kuma sun kwato makamai da dabbobi

Katsina - Gwarazan yan sanda sun samu nasarar daƙile wani kazamin harin yan bindiga da suka addabi jihar, sun sheke guda 5 sun kwato mutanen da aka sace da dabbobi.

Vanguard ta rahoto cewa yan bindigan sun yi yunkurin kai hari kauyukan Kuru da Dangani a karamar hukumar Musawa jihar Katsina.

Sauran abubuwan da yan sandan suka kwato sun haɗa da, bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da zaren alburusai da kuma Mota kirar Gulf III.

Kara karanta wannan

Sama da yan Boko Haram/ISWAP 30,000 sun mika wuya, Gwamna Zulum

Yan sanda
Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun yi kazamar musayar wuta da yan bindiga a Katsina, sun halaka da dama Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Katsina, SP Gambo Isa, shi ne ya bayyana haka yayin da yake nuna wa manema labarai wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato a Hedkwatarsu ranar Jumu'a.

Gambo ya yi bayanin cewa kwamandan yan sanda na yankin Dutsinma ya samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar 10 ga watan Janairu, cewa yan ta'adda da yawa sun farmaki yankin Musawa.

Nan take ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa hanyar da ake tsammanin zasu biyo kusa da kauyen Dangani, suka yi kazamin artabu, yan sanda suka kashe yan ta'adda 5, suka kwato makamai.

Wani harin na daban

SP Gambo ya ce:

"A wannan rana dai da misalin karfe 4:00 na Asuba aka sake kiran kwamandan Dutsinma, nan take ya sake haɗa tawaga suka fukanci wata tawagar yan bindiga kusa da kauyen Dangani, duk a Musawa."

Kara karanta wannan

Nasara: Jiragen yakin Najeriya sun kashe shugabannin yan bindiga da yaransu 37 a Neja

"Lokacin yan bindigan sun sato wani dattijo, Alhaji Sule, daga kauyen Ɗankwari a cikin wata farar mota Gulf III, mai lambar rijista BKR 367 XA."
"Kwamandan da yan tawagarsa suka ja daga da yan bindiga, aka cigaba da artabu, wanda ya tilasta musu tserewa suka bar mutumin da kuma motar anan wurin.

A wani labarin kuma Iyalan Ma'aikacin gwamnati da aka kama da hannu a ayyukan yan bindiga sun yi magana

Ma'aikacin gwamnatin jihar Sokoto, Ladan Ibrahim, na ɗaya daga cikin mutum 45 da aka damƙe kan zargin taimakawa Boko Haram da kuɗaɗe.

Iyalan Malam Ibrahim sun bayyana halin da suka tsinci kan su tun bayan kama jigon da yake ɗaukar nauyin su baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel