‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Mai jego, jariri da wasu mutane a Kaduna a daren Juma'a

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Mai jego, jariri da wasu mutane a Kaduna a daren Juma'a

  • Wasu ‘Yan bindiga sun aukawa Tudun Sarki da Hayin Liman a yankin Zangon Shanu, Zaria a Kaduna
  • Mun samu labarin cewa miyagun sun dauke wata mata mai shayarwa da wani magidanci da ‘dansa
  • Jami’an tsaro na sa-kai sun ceto wasu daga cikin wadanda aka dauke, amma an kuma tsere da wasu

Kaduna - Miyagun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu Bayin Allah yayin da suka shigo wasu kauyuka a yankin Zango a karamar hukumar Sabon Gari.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ‘yan bindigan sun shigo kauyen Tudun Sarki da kimanin karfe 10:00 na daren Juma’a, 10 ga watan Fubrairu 2022.

Wadannan miyagu sun dauke wata mata mai shayarwa da kuma jaririn da ta haifa kafin a farga cikin dare. Tudun Sarki yana kan iyaka ne da ABU dam.

Kara karanta wannan

Gwamnoni da Majalisar Tarayya na neman taba karin albashin da aka yi ta bayan-fage

Bayan sun gama wannan ta’adi sai ‘yan bindigan suka yi gaba, su ka shigo kauyen Hayin Liman. A nan ma sun yi nasarar dauke wani dattijo tare da ‘dan shi.

An dauke Dattijo

Jaridar Legit.ng Hausa ta tabbatar da wannan, inda aka bada sunan wanda aka dauke da Abubakar Garba Aliyu, sai kuma ‘dan sa mai suna Salim Abubakar.

Wasu daga cikin ‘ya ‘yan wannan mutumi sun bayyana cewa mahaifin na su bai dade da dawowa yankin ba, ya taso ne daga unguwar Samuru a kwanan baya.

‘Yan bindiga
Wasu dakaru a bakin aiki Hoto: infoguidenigeria.com
Asali: UGC

An ceto wasu daga cikinsu

‘Yan banga da mutanen gari sun tashi tsaye, aka sanar da jami’an tsaron sa-kai da ke yakin Danmagji-Kufena, wadanda suka yi artabu da ‘yan bindigan.

Wadannan ‘yan banga sun yi kokarin ceto mai jegon da jaririn, sai dai ba a iya kubutar da dattijon da aka dauke tare da matashin ‘dansa a Hayin Liman ba.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Shugaban kungiyar mazauna unguwar Jama’a, Zangon Shanu, Mal, Mohammed Ahmed Muhammad ya tabbatar da cewa an kawo masu hari cikin dare.

Mohammed Ahmed Muhammad ya ce mutanensu sun shirya domin ganin an tsare al’umma. Zuwa yanzu ba mu da tabbacin ko an kashe wasu a dalilin harin.

Mu na da labarin cewa ‘yan sanda sun samu zuwa inda aka yi abin ne da kimanin karfe 12:30 na safe. Daily Trust ta ce kawo yanzu jami’an ba su yi magana ba.

Hare-hare a Zaria

Ba wannan ne karon farko da aka ji shigowar 'yan bindiga wannan yanki ko garin Zaria ba, Kwanaki an ji labarin wata mata da ‘ya ‘yanta uku da aka dauke.

Wannan mata ta na aiki ne da asibitin koyarwa da ke garin Shika. Haka zalika 'yan bindigan sun taba kashe wata ma'aikaciyar ABUTH da suka sace a garin Zango.

Asali: Legit.ng

Online view pixel