Zamfara: 'Yan bindiga sun farmaki kauye saboda kai kararsu ga jami'an tsaro

Zamfara: 'Yan bindiga sun farmaki kauye saboda kai kararsu ga jami'an tsaro

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki jihar Zamfara, sun hallaka mutane biyar a jihar nan take
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, harin ya faru ne daidai lokacin da 'yan bindigan ke fuskantar barazana daga jami'an tsaro
  • An ce sun kai harin horar da mazauna yankin ne bisa kai bayanan 'yan bindiga ga jami'an tsaron yankin

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari da sanyin safiyar ranar Alhamis, sun kashe wasu mutane 5 a garin Rogoji da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara.

Da suke tabbatar da mutuwar mutanen, mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne domin hukunta su bisa ba da bayanai kan ‘yan bindigar ga jami’an tsaro da ‘yan banga, inji rahoton Premium Times.

'Yan bindiga sun farmaki wani kauye saboda kai wa jami'an tsaro kara
Zamfara: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar saboda kai kararsu ga jami'an tsaro | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rogoji kilomita biyu ne kacal daga babban garin Bakura.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kashe DPO da Hafsan Soja a sabon hari a Jibia

Majiyoyi sun ce mazauna yankin sun tallafa wa jami’an tsaro da ’yan banga wajen kai samame kan ‘yan bindiga a yankin Lambar Bakura zuwa Dogon Karfe.

Hamza Abdullahi, wani mazaunin garin Bakura, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari ne da safiyar Alhamis a lokacin da mazauna garin ke shirin sallar asuba.

Ya ce duk da kalubalantarsu da ‘yan banga suka yi, ‘yan bindigar sun shiga cikin garin inda suka kashe mutum biyar.

Na ci gudu da kafa ta kafin na tsira

Wani mazaunin garin Rogoji mai suna Bello Mande da yanzu haka yake neman mafaka a garin Talatan Mafara ya shaida cewa ya ci gudu da kafarsa zuwa Lambar Bakura kafin ya samu motar da ta kai shi Mafara.

A cewarsa:

“’Yan bindigan sun zo ne a kan babura da misalin karfe 5 na safe, suka fara harbi, lamarin da ya ankarar da ‘yan banga a kauyenmu. Idan ba don su ba, 'yan bindigan sun so su yi wa daukacin al'umma kawanya ne. Sun kashe mutum biyar."

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe Bayin Allah, sun hana ‘Yan gari yi masu jana’iza har yau

Hakazalika, ya ba da labarin yadda mazauna garin suka kai bayanan 'yan bindigan ga jami'an tsaro, lamarin da ya tunzura su, kamar yadda jairdar Today ta tattaro.

Ya kara da cewa an yi jana’izar wadanda aka kashen a ranar Alhamis da yamma.

Ya zuwa yanzu, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu ba.

Zamfara, kamar da yawa daga cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya, na fama da matsalar rashin tsaro; garkuwa da mutane da kisa ba gaira ba dalili.

Dubban mutane ne aka kashe sannan aka yi garkuwa da wasu da dama a jihar, tun farkon 2021 zuwa yanzu.

A cikin makonni uku na farkon 2022, akalla mutane 486 aka kashe a fadin Najeriya, sama da rabinsu daga ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da Jihar Neja ne suka aikata barnar.

'Yan fashi sun yi awon gaba da motar kudi, sun kashe 'yan sanda 2

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

A wani labarin, an samu tashin hankali a ranar Alhamis yayin da wasu ‘yan fashi suka farmaki motar kudi a unguwar Idi-Ape da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, The Nation ta ruwaito.

Wasu majiyoyi da ba a tantance ba sun ce ‘yan sanda biyu sun mutu yayin da ‘yan fashin ke harbe-harbe a lokacin da suke gudanar da barnar.

Ba a iya tabbatar da ko ‘yan fashin sun yi nasarar yin awon gaba da motar kudin ba, duk da cewa wasu rahotanni sun ce an tafi da motar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel