Banbaraƙwai: Soyayya mu ke yi, yarinyar da mahaifinta ya ɗirka wa ciki a Bayelsa

Banbaraƙwai: Soyayya mu ke yi, yarinyar da mahaifinta ya ɗirka wa ciki a Bayelsa

  • Yarinyar da mahaifinta ya yi wa ciki a Jihar Bayelsa ta fada wa yan sanda cewa son sa ta ke yi hakan yasa ta amince masa
  • Hakan na zuwa ne bayan yan sanda sun kama mutumin, Baridap Needman, mai shekaru 38 kan zarginsa da keta hakkin 'yarsa
  • Wata kungiyar kare hakkin mata, GRIT, ta yi alkawarin tallafawa yarinyar har ta haihu sannan ta koma makaranta kamar sauran yara

Jihar Bayelsa - Wata yarinya mai shekaru 14, wacce ke ajin karamar sakandare na 3, da mahaifinta ya yi wa ciki ta shaida wa yan sanda cewa soyayya suke yi, Vanguard ta ruwaito.

Yan sanda sun kama mahaifin, Baridap Needman, a Yenizue-Gene a Yenagoa, babban birnin jihar bayan wata kungiyar kare hakkin mata, GRIT, karkashin jagorancin Dise Ogbise ta yi korafi.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Magidanci ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa, ya shaƙe ta har ta mutu

Soyayya mu ke yi, yarinyar da mahaifinta ya ɗirka wa ciki a Bayelsa
Yarinyar da mahaifinta ya yi wa ciki ta ce soyayya suke yi. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A cewar Dise Ogbise da Mrs Mary Accrah Pekeowei, wani makwabcin wanda abin ya faru da ita ne ya tsegunta musu bayan ya gano yarinyar na dauke da juna biyu na watanni biyar kuma mahaifinta ne ya yi cikin.

Tun tana da shekaru 7 mahaifinta ya fara haike mata

Vanguard ta rahoto cewa an gano cewa tun yarinyar tana da shekaru bakwai mahaifinta ya fara taba al'aurarta da yatsunsa.

Lamarin ya kazanta bayan mahaifyar yarinyar ta rasu shekaru kadan da suka gabata inda mutumin ya maye gurbin matarsa da yar sa.

An gano cewa yarinyar tana kwana a kan gado da mahaifinta yayin da kannenta maza biyu suke kwana a kasa.

Yan sanda sun yi mamaki

Jami'an yan sanda na Ekeki inda aka kai rahoton sun yi matukar mamaki lokacin da yarinyar mai dauke da juna biyu ta ce soyayya ta ke yi da mahaifinta da ake zargin.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Yaro mai shekara 13 ya soka wa matashi mai shekara 19 wuka a Borno

Shugaban GRIT, Dise Ogbise, ta tabbatarwa manema labarai a Yenagoa cewa kungiyar za ta yi hadin gwiwa da Ma'aikatar Harkokin Mata domin bawa yarinyar taimakon da ta bukata har ta haihu.

Ta ce:

"Ba bu maganan zubar da cikin an kuma mika kannen ta biyu zuwa ga yan uwansu domin basu kulawa.
"Yarinyar tana hannun gwamnati kuma tana bukatar ta koma makaranta. Fatan ta shine ta zama mawakiya kuma za mu karfafa mata gwiwa."

Daga karshe Mrs Mary Accrah Pekeowei ta yi kira ga al'umma su rika sa ido su kai rahoto idan sun ga ana cin zarafin mata ta kowanne hanya.

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A wani labarin, Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zulum ya sa an kwamushe tsagerun da suka farmaki wata mata saboda ta soki dan majalisa a Facebook

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Online view pixel