Magidanci ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa, ya shaƙe ta har ta mutu

Magidanci ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa, ya shaƙe ta har ta mutu

  • Rundunar yan sanda ta yi ram da wani makanike dake da 'yaya bisa zargin halaka budurwarsa da ta kawo masa ziyara
  • Rahoto ya nuna cewa ana zargin mutumin da lakaɗa wa budurwarsa dukan tsiya, kuma ya shake mata wuya har ta mutu
  • Iyalan mamaciyar sun bayyana cewa mutumin ne ya gayyaci yar uwarsu, kuma suna zargin cewa shi ne ya kashe ta

Ondo - Hukumar yan sanda reshen jihar Ondo na cigaba da bincike kan wani magidanci ɗan shekara 40, Olasunkami Oluwole, bisa zargin shaƙe budurwarsa har ta mutu.

Vanguard ta rahoto cewa magidancin mai aikin kanikanci, ya aikata wannan danyen aikin ne a yankin Oke Igbo dake jihar Ondo.

Oluwole, mahaifin yara biyu, ya gayyaci masoyiyarsa, Biola Soyinka, wacce ke zaune a jihar Legas, ranar 3 ga watan Janairu, 2022.

Kara karanta wannan

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

Jihar Ondo
Magidanci ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa, ya shaƙe ta har ta mutu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa magidancin ya sauke masoyiyar tasa a wani wuri daban da gidansa dake yankin Oke Igbo saboda gudun matarsa.

Sai dai bayan mutuwar budurwan, mutumin ya kira ƙanwarta domin ya sanar da ita cewa Biola ta mutu.

Ya iyalanta suka ɗauki lamarin?

A cewar yayan marigayya Biola, Akeem Jinadu:

"A ranar 16 ga watan Janairu, Oluwole, ya kira mu a waya ya sanar da mu cewa ƙanwata ta mutu. Da muka tambaye shi me ya faru? Sai yace mana ta jigata bayan ta yanke jiki ta faɗi da safiyar Lahadi."
"Oluwole ya faɗa mana cewa da ya garzaya da ita Asibiti, sai Likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa. Da muka nemi ya kawo mana gawarta Legas, sai ya bukaci kuɗin mota a wurin mu."

Kara karanta wannan

Na gwammaci yashe teku: Cece-kuce yayin da budurwa ta rokon saurayi ya aureta

Shin dagaske yanke jiki ta yi ta faɗi?

Jinadu ya ƙara da cewa sabanin yadda ya shaida mana, bayan yan sanda sun damƙe shi, mun ga tabon duka a jikinta yayin da muka je ɗauko gawarta.

"Daga yanayin gawarta muka tabbatar ba faɗuwa ta yi ba, sai dai tabban da muka gani a jikinta da wuyanta ya tabbatar da duka ta sha kuma aka shaƙe ta har ta mutu."

Rahoto ya nuna cewa hukumar yan sanda ta miƙa lamarin ga sashin binciken manyan laifuka dake Akure, domin tsananta bincike.

A wani labarin na daban kuma Mahaifiyar Ɗan Majalisa a Kano da Yan Bindiga Suka Sace Ta Kubuta Bayan Biyan Miliyan N40m

Mahaifiyar kakakin majalisar dokokin jihar Kano ta shaki iskar yanci daga masu garkuwa bayan biyan makudan kuɗi a matsayin fansa.

Honirabul Ali Ɗanja, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar, yace maharan sun saki mahaifiyarsa a wata karamar hukuma dake Jigawa.

Kara karanta wannan

Tanko Yakasai: 'Yan Arewa ba sa tsinana komai a Najeriya, a ba 'yan kudu mulki a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel