Zulum ya sa an kwamushe tsagerun da suka farmaki wata mata saboda ta soki dan majalisa a Facebook

Zulum ya sa an kwamushe tsagerun da suka farmaki wata mata saboda ta soki dan majalisa a Facebook

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi umurnin damke tsagerun da suka suburbudi wata mata saboda ta soki dan majalisa a Facebook
  • An rahoto cewa matar mai suna Fadila ta soki Ahmad Satomi Grema, dan majalisa mai wakiltan mazabar jere wanda hakan ne ya sa suka kai mata farmaki a shagonta
  • Tuni dai jami'an tsaro suka cika umurnin gwamnan na kamo masu laifin, inda shi kuma Satomi ya nesanta kansa da su

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi umurnin kama yan daban da suka suburbudi Fadila Abdulrahman, wata mazauniyar jihar, kan wani wallafa da ta yi a Facebook.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Fadila ta soki Ahmad Satomi Grema, dan majalisa mai wakiltan mazabar jere a wallafar tata.

Kara karanta wannan

Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara

Zulum ya sa an kwamushe tsagerun da suka farmaki wata mata saboda ta soki dan majalisa a Facebook
Zulum ya sa an kwamushe tsagerun da suka farmaki wata mata saboda ta soki dan majalisa a Facebook Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cikin wani bidiyo da ke yawo, an gano yan daban wadanda aka ce masu biyayya ne ga dan majalisar, suna marin Fadila a shagonta da ke filin wasa na Shehu Sanda Kyarimi a Maiduguri.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan daban dauke da sanduna da sauran makamai sun rushe shagon Fadila bayan sun tarwatsa mata kayayyakinta.

Wata majiya ta tsaro ta sanar da The Cable cewa an gano yan daban da ke cikin bidiyon kuma an kama su.

Majiyar ta ce:

“A daren jiya, mai girma gwamna ya yi fushi sosai. Yana adawa da dabar siyasa, bugu da kari na daren jiya ba wai dabar siyasa bane kawai ya kasance cin zarafin jinsi a jihar. Gwamnan ya yi umurci kwamishinan yan sanda da ya tabbatar da kamun a daren jiya kuma an aiwatar da umurninsa.”

Kara karanta wannan

APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP

Gwamnan ya kuma bukaci jami’an tsaro da su bincika sannan su hukunta wadanda suka aikata laifin daidai da doka.

Ahmad Satomi ya yi martani

A wata sanarwa da ya fitar, Satomi ya nesanta kansa daga yan dabar, cewa masu laifin ba shi suke wa aiki ba.

Sanarwar ta ce:

“Ni, Hon Ahmed Satomi, dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Jere ya jihar Borno ina danasanin cewa an ja hankalina zuwa wani ikirari ko zargi cewa ni ke da alhakin rushe wani wajen siyar da abinci a filin wasa a Maiduguri wanda aka fi sani da ‘Zuhura restaurant’.
“Eh, an rahoto cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba cikin keken adaidaita sun kai farmaki da kona wajen siyar da abincin da ake magana a kai saboda wani dalili nasu.
“Ina son janye kaina daga wannan aiki, duba ga cewa bisa tarihi ni mutum ne mai son ci gaban tattalin arziki ta hanyar dogaro da kai, tun kafin da ma bayan na zama dan majalisar tarayya mai wakiltan mutanen kirki na karamar hukumar Jere.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

“Abun damuwa ne cewa wasu da suka zabi zama yan adawa da ake biya don sukar Hon Satomi saboda dalili wata fa’ida sai kawai su je shafukan sadarwarsu musamman shafukan Facebook suna sukar shi."

Saura kiris wasu 'yan siyasar Najeriya su zama araha gama-gari, Shehu Sani ya fadi dalili

A wani labari na daban, Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna, ya ce zaben 2023 zai sauya makomar wasu ‘yan siyasar Najeriya da dama.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa galibin mutanen da suke daukar kansu a matsayin alloli saboda karfin da suke dashi na mulki, bayan sauka daga mulkin za su rasa duk wata kariya da suke takama da ita.

Sani wanda ya fadi haka a Facebook a ranar Lahadi, 23 ga Janairu, ya yi hasashen cewa, irin wadannan ake ganin sun fi karfin kowa kuma ba za a taba taba su ba saboda isa da yawan jami'ai za su zama araha a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel