Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

  • Fitaccen mawakin Najeriya, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya ce ya tuba, ya dena yi wa yan mata ciki
  • Mawakin ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo ya bazu a dandalin sada zumunta yayin wani biki na Idoma International Carnivial
  • Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan bidiyon duba da cewa an san shi da 'yan mata a kalla uku da suka haifa masa yara

Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

Kara karanta wannan

Alheri danko ne: Bidiyon mai tallan pure water yana raba wa fursunoni kudi ya ja hankalin jama'a

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba
2Baba: Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki. Hoto: Innocent Idibia

A cikin faifan bidiyon, Shugaban kamfanin Hypertek Digital ya yi magana ne cikin harshen Pidgin.

Ya ce:

"Na lura wasu 'yan mata suna tsoron su yi min magana a can wurin.
"Kada ku ji tsoron yin magana fa. Na dena yi wa mata ciki haka nan, na dena.
"Ka tambayi kowa, za su fada maka. Ni yanzu mutum ne mai gaskiya. Ba na yin hakan a yanzu."

Da suke martani game da wannan bidiyon, ma'abota amfani da kafafen sada zumunta sun yi tsokaci masu ban dariya:

hes_black ya ce:

"Baba don Allah kada ka yi murabus. Ijeoma a unguwar mu tana wahal da mutane kuma tana kaunar ka. Ka yi mata ciki kafin ka yi murabus."

_chynwe ta rubuta:

"A yanzu da lokaci na yazo ka ke son yin ritaya. 2 baba hakan fa babu kyau. Annie, wasa fa na ke yi."

Kara karanta wannan

Duniya ba tabbas: Bidiyon motar alfarma da gida da wata miloniya ta mutu ta bari babu magada, har sunyi tsatsa

Ezeqwesiri ya ce:

"Bai ce ya yi ritaya ba. Ya ce bai cika yin cikin kamar yadda ya saba yi a da ba. Hakan na nufin duk da haka zai iya yi jefi-jefi."

mrpresidennnt ya yi tambaya:

"Kudin makaranta da abinci jarirai sa'ar ka ne?"

princessbase_ ta ce:

"Diapers da kudin makaranta za su saka ka saduda."

honey_mixwealth1 ya rubuta:

"Ranka ya dade, Kada ka yi watsi da baiwar ka."

wonderboyvibes:

"Baban kasashe da dama."

shemisjewelry ta ce:

"Ban san yana raha haka ba ... mara gaskiya kuma mai gaskiya."

folabialli ya ce:

"Ya yi murabus ya ajiye igiyar kyaftin ya bar wa Tee Billz, yanzu shine gogan."

tinywale ya ce:

"2Baba babu bukatar ka kusanci wata mace ma kafin ta yi ciki! Kawai ta jefa tawul dinka cikin mutane yanzu, dole yan mata 2 su dauki ciki."

Saboda kusancin mu, mahaifina na fara kira ranar da na rasa budurcina, Mawaƙi Kizz Daniel

Kara karanta wannan

Ina fatan ninka yawan 'ya'ya na, Magidanci mai yara 9 da ke cikin tsananin talauci da rashi

A wani labarin daban, mawakin Najeriya, Daniel Anidugbe wanda aka fi sani da Kizz Daniel ya bayyana yadda ya fara kiran mahaifinsa a ranar da ya rasa budurcinsa lokacin yana da shekaru 21, The Punch ta ruwaito.

Yayin wata tattaunawa da mujallar TheWill Downtown ta yi da shi, an tambayeshi irin kusancin da ya ke da shi da mahaifinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel