Wani mutum ya yi garkuwa da yar makwabcinsa, ya kashe ta bayan ya karbi kudin fansa a Kaduna

Wani mutum ya yi garkuwa da yar makwabcinsa, ya kashe ta bayan ya karbi kudin fansa a Kaduna

  • Wani mutum ya yi garkuwa da yar makwabcinsa sannan kuma ya kashe ta bayan ya karbi kudin fansa sama da naira miliyan uku
  • Mahaifin yarinyar mai suna Asmau ya bayyana cewa a lokacin da yarinyar ta bata ya sanar da yan sanda
  • Sai wadanda suka yi garkuwa da ita suka kira shi tare da neman ya biya kudin fansa inda ya basu, bayan ta shafe kwanaki 42 sai suka kuma kiranshi tare da fada masa cewa sun kashe ta

Kaduna - Al'umman garin Zariya da ke jihar Kaduna na alhinin kisan wata yarinya yar shekaru takwas mai suna Asmau, wacce ake zargin makwabcinta da yin garkuwa da ita sannan daga bisani ya kuma kashe ta.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa, wani makwabcin su Asmau ne ya yi garkuwa da ita a ranar 9 ga watan Disamba, 2021 sannan ta shafe kwanaki 42 a hannunsu.

Kara karanta wannan

Na san zafin haihuwa: Makashin 'yar makaranta Hanifa ya bayyana adadin 'ya'yansa

Wani mutum ya yi garkuwa da yar makwabcinsa, ya kashe ta bayan ya karbi kudin fansa a Kaduna
Wani mutum ya yi garkuwa da yar makwabcinsa, ya kashe ta bayan ya karbi kudin fansa a Kaduna Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi, mahaifinta, Alh Shuaibu Wa’alamu ya fadawa manema labarai a Zariya a karshen mako yadda aka sace ta.

Ya ce:

"An yi garkuwa da diyata a ranar 9 ga watan Disamba lokacin kuma lokacin da ta ki dawowa gida, na kai kara ofishin yan sanda.
"Bayan yan wasu kwanaki, sai wadanda suka yi garkuwa da ita suka fara kiran lamba na sannan suka nemi na biya miliyan N15. Amma sai muka sasanta kuma na fara basu naira miliyan biyu.
"Sun karbi kudin a yankin Rigasa da ke Kaduna. Daga bisani, sai suka sake kirana sannan suka nemi na sake basu miliyan N1.45 kafin su saki diyata.
"Ban yi gardama ba. Amma na basu kudin.
"Sai dai kuma bayan na biya kudin fansar kamar yadda suka bukata a ranar 19 ga watan Janairu, sai suka kirfani don fada mani cewa sun kashe ta sannan suka kashe wayar.

Kara karanta wannan

Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu

"Kun ga tun farko, ina ta bin wadanda suka sace ta sannan ina yin abun da suka bukata saboda tsoron rasa ta. Yanzu sun kashe ta.
"Na san wadanda suka sace ta da kashe ta. Suna kewaye da mu. Ina da hujja mai karfi. Na fada ma yan sanda. Kuma suna kan abun. A zahirin gaskiya ma, an kama wadanda ake zargin."

Aminiya ta rahoto cewa mahaifin yarinyar ya ce a yanzu haka dai jami’an ’yan sanda masu yaki da muggan laifuka na IRT ne suka kama wanda ake zargin domin fadada bincike.

Sai dai kuma, rundunar yan sanda bata tabbatar da labarin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano

A wani labarin kuma, mammalakin makarantar Noble Kids School dake jihar Kano ya shiga komar yan sanda kan laifin garkuwa da kashe dalibar makarantarsa, Hanifa Abubakar yar shekara biyar.

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

Yan'uwanta sun bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka je gidan iyayenta jajanta musu lokacin da aka sace ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel