Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

  • Shugaban makarantar su Hanifa ya bayyana irin gubar da ya bai wa dalibarsa ta sha nan take ta mutu a gidansa
  • Ya bayyana cewa, ya sayi gubar bera ta N100 ne ya zuba mata a abinci ta ci, lamarin da ya ba jama'a tausayi
  • An ruwaito yadda wani shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko ya hallaka yarinya 'yar shekara biyar bayan sace ta

Kano - Shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School, Kawana, Kano, Abdulmalik Tanko, ya bayyana yadda ya yi amfani da gubar bera na Naira 100 wajen kashe daya daga cikin dalibansa.

A baya an ruwaito yadda wasu miyagu suka yi garkuwa da Hanifa Abubakar, ‘yar shekaru biyar yayin da take kan hanyarta ta dawowa daga makarantar Islamiyya a watan Disamba kuma suka yi mata kisan gilla.

Kara karanta wannan

Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu

JIhar Kano: Malamin da ya kashe dalibarsa ya magantu
Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tanko dai ya bukaci iyayen yarinyar da su biya kudin fansa Naira miliyan 6 amma ya shiga hannu yayin da yake kokarin karbar kudin fansan, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kasa bayyana cewa ya kashe yarinyar da ya sace lokacin da yake cinikin kudin fansa da iyayenta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin da aka kama shi, an kawo shi hedikwatar ‘yan sandan Kano a ranar Juma’a, inda ya shaida wa manema labarai cewa ya sanya wa yarinyar gubar bera da ya saya kan kudi Naira 100.

Garin rage mata hanya, an sace yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano

An sace wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar a unguwar Kawaji da ke Kano a ranar Asabar.

Masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da ita a cikin babur din dai-daita sahu yayin da suka yaudare ta da sunan rage hanya.

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Yahaya Bello ya sanar cewa ya shiga jerin masu son gadon kujerar Buhari

Daily Nigerian ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da karfe 5 na yamma lokacin da yarinyar da sauran yaran unguwar suke dawowa daga makarantar islamiyya.

Kawunta, Suraj Zubair ya ce:

A yau Juma'a, Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi rikici a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano, yayin da Fatima Maina, mahaifiyar Haneefa Abubakar, ‘yar shekara biyar da aka ce malaminta ya kashe, ta hango mutumin da ya yi garkuwa da diyarta.

A baya an ruwaito yadda aka kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kawana, Kano, dangane da lamarin.

Tun a watan Disamba ne aka yi garkuwa da Haneefa, kuma masu garkuwar suka bukaci a biya ta Naira miliyan 6 a matsayin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel