Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu

Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu

  • Yan Najeriya na cigaba da alhini da bayyana takaici bisa abinda ya faru a jihar Kano na kisan yarinya da shugaban makaranta yayi
  • Malaman addini, yan siyasa da yan fafutuka sun yi ga gwamnati ta dau matakin da ya kamata kan wadannan makasa
  • Mahaifin yarinya ya bayyana irin halin da ya shiga sakamakon kashe masa diya da ta tafi makarantar Alkur'ani

Kano -Mahaifin Hanifa Abubakar, yarinya yar shekara biyar da Malamin makaranta ya sace kuma ya kashe ya bayyana alhininsa bisa abinda ya afkawa shi da iyalansa.

Wannan ya biyo bayan yunkurin dukan da mahaifiyar Hanifa ta yiwa makashin gaban jami'an tsaro.

A dan karamin tsokacin da mahaifin ya yiwa yan jarida yana kuka, mahaifin ya bayyana cewa ya rungumi kaddara amma ba zai taba mantawa da abinda akayiwa diyarsa ba.

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

Ya bayyana irin halin bakin cikin da yake ciki amma ya yi tawakkali ga Allah.

Yace:

"Na tsinci kaina cikin halin bakin ciki kan wannan abin da ya faru, gaskiya sai dai in godewa Allah akan wannan abu saboda ban wuce wannan abu ya sameni ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kuma an ce duk mai rai mamaci ne saboda haka na yi tawakkali amma har in mutu ba zan manta da abin a zuciyata ba, mutanen da suka yi wannan abu basu yi min adalci ba, ba su yiwa duniya adalci ba.
Yarinya ta dawo daga makarantar Alqur'ani, Allah ya saka min da Alkhairi."

Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu
Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu Hoto: Daily Trust
Asali: Instagram

Ya gode jami'an tsaro bisa kokarinsu

Mahaifin Hanifa ya karashe jawabinsa da godewa jami'an hukumar DSS da yan sanda suka bi diddigin wannan lamari har aka gano makasan.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa a 2021: Yadda hauhawar farashin kayayyaki ya kasance a kowane wata

Ina godewa jami'an tsaro na kasar nan ga baki daya wadanda suka yi kokari wajen gani wannan abu. Mun gode bisa kokari, Allah ya saka muku da Alkhairi

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel