Na san zafin haihuwa: Makashin 'yar makaranta Hanifa ya bayyana adadin 'ya'yansa

Na san zafin haihuwa: Makashin 'yar makaranta Hanifa ya bayyana adadin 'ya'yansa

  • Abdulmalik Tanko, makashin yarinya 'yar shekara biyar a Kano ya bayyana adadin 'ya'yan da yake dasu
  • Ya ce shi ma uba ne, ya san zafin haihuwa don haka ya san bai kyautawa iyayenta ba ko kadan a rayuwa
  • Ya kuma basu hakuri kan abin da ya aikata, inda ya bayyana nadama da aikin da ya aikata, tare da cewa ya san doka

Kano - Shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kano, Abdulmalik Tanko ya bayyana cewa shi ma yana da ‘ya’ya mata uku.

Tanko, wanda ya yi garkuwa da Hanifa Abubakar mai shekaru biyar a watan Disamba 2021, kuma daga baya ya kashe ta, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ranar Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Har zubar da hawayen ƙarya: Mai makarantar su Hanifa ya yaudare mu yayin da ya zo jajen ɓatar ta, Kawun Hanifa

Mashekin Hanifa ya magantu
Ya san zafin haihuwa: Shugaban makarantar da ya kashe Hanifa ya bayyana yawan 'ya'yansa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A baya an ruwaito yadda aka yi garkuwa da Hanifa a lokacin da take kan hanyarta ta dawo daga makarantar Islamiyya a watan Disamba.

Tanko dai ya bukaci iyayen yarinyar da su biya kudin fansa Naira miliyan 6 wanda a garin karbar kudin fansan ne jami'an tsaron Najeriya suka yi aikinsu a kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin ya shiga hannu, lokacin da yake shirin karbar kudin fansan bai bayyana ya kashe yarinyar ba har sai da ya shiga hannu.

Da aka tambaye shi ko yana da 'ya'ya, ya bayyana cewa:

“Ina da ‘ya’ya mata uku… Ina matukar nadama, ko da lokacin da yarinyar nan take mutuwa, na yi matukar kaduwa. Matsalar kudi ce ta sa na yi’; Masu gida suna bi na bashin haya.
"Abu na farko da nake so a yanzu shine, kawai ina so in nemi afuwar wadannan iyayen. Gaskiya, na yi nadama da abin da na yi musu, na yi nadamar abin da na yi musu. Na kashe 'yarsu don haka su yi hakuri.

Kara karanta wannan

Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu

“Wannan rayuwa ce, rayuwa abu ce mai daraja. Na san dukkan dokoki."

Ya kuma ba da labarin yadda ya kashe yarinyar da bata masa komai ba tare da bayyana abin da ya yi amfani da kudin da ya karba a wurin iyayenta.

Tanko ya ce ya yi amfani da N70,000 daga cikin N100,000 da ya karba daga iyayen Hanifa wajen biyan albashin ma’aikatansa.

A baya dai Tanko ya saci Hanifa ne a watan Disamba, inda ya yaudare ta da sunan zai rage mata hanya lokacin da take dawowa daga Islamiyya, inji rahoton Daily Nigerian.

Me yasa ka kashe ta: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta

A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi rikici a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano, yayin da Fatima Maina, mahaifiyar Haneefa Abubakar, ‘yar shekara biyar da aka ce malaminta ya kashe, ta hango mutumin da ya yi garkuwa da diyarta.

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

A baya an ruwaito yadda aka kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kawana, Kano, dangane da lamarin.

Tun a watan Disamba ne aka yi garkuwa da Haneefa, kuma masu garkuwar suka bukaci a biya ta Naira miliyan 6 a matsayin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel