Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba

Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba

  • Sanata Orji Uzor Kalu, ya yiwa wadanda suka riga suka ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa gabannin babban zaben 2023 wankin babban bargo
  • Kalu ya ce duk wanda ya fito karara ya bayyana kudirinsa na yin takarar kujerar tun yanzu bai san me yake yi ba
  • Tsohon gwamnan na jihar Abia ya ce shi bai yarda da shugabancin Igbo ba, amma ya yarda da shugaban Najeriya na tsatson Igbo

Abuja - Mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya caccaki wadanda suka riga suka ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa gabannin babban zaben 2023.

Dan siyasar wanda ke wakiltan yankin Abia ta arewa a majalisar dattawan ya bayyana cewa wadannan mutane basu san me suke yi ba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba
Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba Hoto: Senator orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Kalu ya kuma bayyana cewa shi bai yarda da shugabancin Igbo ba, amma ya yarda da shugaban Najeriya na tsatson Igbo, kamar yadda ya bayyana cewa idan aka mika shugabancin kasar zuwa yankin kudu maso gabashin kasar, yana da abun da ake bukata na neman kujerar.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga yan jarida a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, Kalu ya ce bai fara tuntuba ba gabannin ayyana kudirinsa na neman takarar shugaban kasa a hukumance.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"A zahirin gaskiya suna yunkurawa amma ba su san me suke yi ba, wanda ya san abun da yake yi zai so yiwa Najeriya adalci, sannan ya yiwa al'umma da yanayin adalci, saboda jam'iyya ba ni ko ku kafofin watsa labarai bane ke da ita.
"Wannan jam'iyya mallakar yan Najeriya da mambobin APC ne. APC kadai ce za ta iya yanke shawara irin wannan a babban taro mai zuwa kan inda za a mika tikitin shugaban kasa. Idan suka mika shi kudu maso gabas ina da duk abun bukata a shugaban kasa nagari."

Kara karanta wannan

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

Game da matsayarsa kan batun cewa zagayen Igbo ne, Kalu ya ce:

"Ya ma wuce, Na yarda cewa mu yakamata mu samar da shugaban kasa na gaba kuma hakan zai faru. Bana bukatar matsawa, Dole ne in tura tare da sauran yankuna."

Rahoton ya kuma ce da aka tambaye shi ko ya fara tuntuba sai ya ce:

"A'a saboda lokaci bai yi ba tukuna."

Kan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Talata, Kalu ya ce:

"Wannan abu ba shine karo na farko da nake zuwa ganin shugaban kasar ba, fadar shugaban kasa wuri ne da mutane ke zuwa da rana, na je da daddare ne domin guje ma kafofin labarai. Ina zuwa chan akai-akai abu ne na cikin gida kuma na je don tattauna lamuran kasa, lamarin tsaro, lamarin ci gaban kasarmu da kuma lamarin zabe. Tattaunawar ta cimma nasara sosai kuma da daddare aka yi ta, shi ya sa ka zo ka yi min kwanton bauna?"

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Da aka tambaye shi ko ya sanar da shugaba Buhari aniyar tsayawa takarar shugaban kasa, Orji Kalu ya ce:

"Shin jam’iyyar ta mika tikitin shugaban kasa na 2023 zuwa Kudu maso Yamma, na fada muku a baya lokacin da jam’iyyar ta mika shi zuwa kudu a hukumance. Na fada muku shiyyoyi biyu da ba su dandana shugabancin kasa ba su ne kudu maso gabas da arewa maso gabas, da zarar sun mika shi ga kowanne daga cikinsu ina da karfin da zan yi birgima kamar guguwa.”

2023: Orji Kalu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce ya ji dadi sosai

A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kalu ya bayyana cewa sun tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasar tare da shugaban kasar. Ya kuma ce ya bar Buhari cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel