2023: Orji Kalu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce ya ji dadi sosai

2023: Orji Kalu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce ya ji dadi sosai

  • Bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu ya sa labule da shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Sun yi ganawar ne cikin sirri a fadar shugaban kasa a daren ranar Talata, 18 ga watan Janairu
  • Kalu ya kuma bayyana cewa sun tattauna muhimman batutuwa kafin ya bar shugaban kasar cikin koshin lafiya

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kalu ya bayyana cewa sun tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasar tare da shugaban kasar. Ya kuma ce ya bar Buhari cikin koshin lafiya.

2023: Orji Kalu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce ya ji dadi sosai
2023: Orji Kalu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce ya ji dadi sosai Hoto: Senator orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Abia a wallafar da yayi a shafinsa na Facebook ya kuma bayyana cewa ya yi farin ciki sosai da matsayin da shugaban kasar ya dauka kan abunda suka tattauna.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hadimin Buhari ya bayyana adawarsa ga tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa

Dan siyasar na daya daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da suka bayyana aniyarsu na neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Kalu ya rubuta a shafin nasa:

"A daren yau, na ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasa kuma na gamsu sosai da abubuwan da muka tattauna.
"Na bar shi da misalin karfe 10:00 na dare kuma cikin koshin lafiya. Muna duba ga Najeriya mai inganci."

Ba zan taba sukar Tinubu ba, aboki na ne: Orji Uzor Kalu

A wani labarin, mun ji cewa tsohon Gwamnan jihar Abia kuma mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya wanke kansa daga rahotannin cewa yana zagin jagoran All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

Zaku tuna cewa Kalu a wata hirar da yayi ya ce shirya yake da ya 'kara da Tinubu a zaben fidda gwanin kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Martani kan rahotannin cewa ya zagi tsohon gwamnan jihar Legas, Kalu ya yi magana ta ofishin yada labaransa inda yace:

"Ba zamu taba sukar Tinubu ba. Na fadawa yan Najeriya cewa zan yi takara da Tinubu idan aka baiwa yankin kudu tikici. APC jam'iyyar demokradiyya ce dake baiwa kowani mamba da ya cancanta daman zabe kuma a zabesa."
"Ba jam'iyyar wani mutum daya bace. Idan nace zan yi takara da Tinubu, hakan bai nufi na zageshi. Ba zan iya zaginsa dan wani dalili ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel