Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

  • Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, ya bayyana hanyoyin da za a bi domin yakar cin hanci da rashawa cikin nasara a kasar
  • IBB ya ce dole ne a gano tushen cin hanci da rashawa kafin a iya maganceta, don haka ya shawarci gwamnati da ta cire hannunta a wasu harkoki don cimma nasara
  • Ya ce ya sha bayar da shawarwari kan haka amma mutane basa son ji saboda kawai abun ya fito daga gare shi

Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana yadda za a iya raba kasar da cin hanci da rashawa.

A wata hira da Trust TV, tsohon dan siyasar ya bayyana cewa ya yi ritaya daga siyasa amma har yanzu yana da ra'ayi a abubuwan da ke faruwa a bangaren siyasa.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB
Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB Hoto: Daily Post

Ya ce:

"Eh nayi ritaya daga siyasa; bana siyasa amma har yanzu ina da ra'ayi a abubuwan da ke faruwa a siyasar saboda wannan ce kasata, bani da wata kasa, dole na samu ra'ayi a abun da ke wakana."

Sai dai kuma, ya sake bayar da wasu muhimman shawarwari kan yadda gwamnati za ta yi nasara a yaki da cin hanci da rashawa.

IBB ya ce:

"Na bayar da wani shawara amma saboda ya fito daga gareni, babu wanda ke son shi, babu wanda ke son jin shi: A gano wuraren cin hanci da rashawa sannan a magance su daga tushe. Na karanta daya daga cikin jaridu inda alkali ke korafin cewa ba a biyansu albashi mai kyau kuma hakan tabbataccen tushe ne na cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Ina fatan ninka yawan 'ya'ya na, Magidanci mai yara 9 da ke cikin tsananin talauci da rashi

"A duk inda kake da tsari da ke da masu jan ragama da yawa dole za a samu cin hanci da rashawa. Don haka, abun da muke kokarin yi, muna shawartan gwamnati da kada ta shiga cikin abubuwa kamar sarrafa kayayyaki; duk wani abu da ya shafi sai na zo wajenka kuma za ka rika tunanin kana yi mani alfarma ne, don haka wata kila in rama shi, haka abin yake."

Ya ci gaba da cewa:

"Kuma wannan ne yasa muka billo da tsarin yantar da tattalin arziki; ba ka bukatar lasisi don samun maki babba a gyadarka ko koko ko auduga ko ma dai menene; ba ka bukatar zuwa babban bankin kasa ko zuwa bankuna don samun kudin waje.
"Akwai wajen canjin kudi, suna kafa shi a yankunan kasuwa, inda cikin sauki za ka je ka same shi; don haka ya zama dole a gano tushen cin hanci da rashawa sannan a magance shi."

Kara karanta wannan

Benue: Ɗan shekaru 44 ya cire ƴaƴan marainansa da kansa don daƙile tsabar sha'awarsa

Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB

A baya mun ji cewa tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) ya bayyana dalilin da yasa bai sake aure ba tun bayan mutuwar matarsa, Hajiya Maryam Babangida.

IBB, wanda shekarunsa 80 yanzu ya bayyana hakan a hirarsa da sabuwar gidan talabijin Trust TV.

Allah ya yiwa Hajiya Maryam Babangida rasuwa ranar 27 ga Disamba, 2009, tana mai shekaru 61.

Asali: Legit.ng

Online view pixel