Benue: Ɗan shekaru 44 ya cire ƴaƴan marainansa da kansa don daƙile tsabar sha'awarsa

Benue: Ɗan shekaru 44 ya cire ƴaƴan marainansa da kansa don daƙile tsabar sha'awarsa

  • Terhemen Anongo, mutum mai shekaru 44 mazaunin garin Gboko a jihar Benue wanda ya cire 'ya'yan marainansa duka biyu
  • Kamar yadda ya sanar, ya yi hakan ne saboda ba shi da aure kuma hakan zai ba shi damar bautawa Ubangiji yadda ya dace
  • Mai turin baron wanda ya bar jami'a bayan fara karatun likitanci, ya cire dan marainansa 1 a shekarar da ta gabata inda ya kusa rasa ransa

Gboko, Benue - Terhemen Anongo, wani mutum mai shekaru 44 kuma mazaunin Gboko a jihar Benue, ya cire 'ya'yan marainansa saboda ya tserewa tsabar sha'awarsa.

Anong, wanda ya bar karatun likitanci, ya yi ikirarin cewa wannan hukuncin zai ba shi damar bautawa Ubangiji yadda ya dace, Daily Trust ta ruwaito.

Benue: Ɗan shekaru 44 ya dandaƙe kansa domin kaucewa sha'awa
Benue: Ɗan shekaru 44 ya dandaƙe kansa domin kaucewa sha'awa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, a shekarar da ta gabata, ya cire daya daga cikin 'ya'yan marainansa da kansa kuma hakan yasa ya kusa zama sanadin rasa rayuwarsa.

Ya bayyana, inda yayi suna a watan Maris bayan ya yi wa kansa aikin, wanda hakan yasa ya dinga zubar da jini babu kakkautawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taimakon gaggawan da wadanda suka san abinda ya aikata suka kai masa ne ya tseratar da shi saboda yadda masana kiwon lafiya suka dinga bashi kulawa.

Anongo, wanda ya bar jami'ar Ibadan fannin koyon ilimin likitanci saboda rashin lafiyarsa, ya ce dandaka ce kadai ta dace da shi a addinance saboda bashi da aure, kuma hakan zai ba shi damar bautawa Ubangiji da kyau.

A yayin zantawa da manema labarai a Makurdi a ranar Lahadi, tsohon dalibin wanda ya zama mai turin baro a halin yanzu, ya ce:

"Na je na cire dayan dan maraina na saboda addinin da nayi imani da shi. Na cire a ranar Litinin. Na farkon na samu matsala, amma na koyi darasi daga shi, na cire na biyun lafiya kalau. Wani yana zuwa inda yake wanke min.

"Ina lafiya kalau. Babu matsala. Ina jiran lokacin da mikin zai warke ta yadda zan iya kwance dinkin."

Kungiya ga Ortom: Ka mayar da hankali wurin biyan albashi a Benue, maimakon matsawa Buhari

A wani labari na daban, kungiyar matasan Tiv ta fadin duniya ta yi kira ga gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da ya mayar da hankali wurin dawo da sunansa da bunkasa walwalar ma'aikata a jihar fiye da "amfani da sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a kanun labarai".

Shugaban kungiyar matasan Tiv, Honarabul Mike Msuaan, ya fadi hakan ne yayin mayar da martani ga amsar da Ortom ya bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan tattaunawa da ChannelsTV.

Daily Trust ta ruwaito cewa, sanannen abu ne cewa gwamna Ortom ya kawo wa jihar Benue ci bayan shekara 20 sannan ya zama kadangaren bakin tulu ga cigaban jihar, kungiyar tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel