Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB

Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB

  • Janar Ibrahim Babangida ya sake hira da yan Najeriya kan abubuwa da dama, ciki har da rashin aurensa
  • Babangida, tsohon shugaban kasan mulkin Sojan Najeriya ne wanda yayi mulki tsakanin 1985 da 1993
  • Bayan sama da shekaru 12 da mutuwar matarsa Maryam Babangida, har yanzu tsohon Sojan bai yi aure ba

Minna - Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) ya bayyana dalilin da yasa bai sake aure ba tun bayan mutuwar matarsa, Hajiya Maryam Babangida.

IBB, wanda shekarunsa 80 yanzu ya bayyana hakan a hirarsa da sabuwar gidan talabijin Trust TV.

Allah ya yiwa Hajiya Maryam Babangida.rasuwa ranar 27 ga Disamba, 2009, tana mai shekaru 61.

Ta rasu ne a jami'ar California dake Amurka bayan fama da cutar kansa.

Yayinda aka tambayesa kan shin me yasa bai yi aure tun lokacin ba, yace:

Kara karanta wannan

Labarin cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci faretin tunawa da Sojojin da suka mutu faggen fama

"A'a, ban yi ba. Kuma da kun sani. Yan jarida na bibiya ta. Zabi na kenan; na yanke shawaran karramata ta hanyar kin yin wani aure."

Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB
Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel