Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

  • 'Yan ta'adda sun tare mota dankare da fasinjjin Legas a jihar Imo inda suka tasa keyarsu zuwa cikin daji
  • Lamarin ya faru a yankin Obiohuru da ke karamar hukumar Isiala Mbano da ke jihar a ranar Talata da ta gabata
  • Motar ta na dauke da fasinjoji kuma ta baro Uyo, miyagun sun tare su tare da sace su inda suka bar motar dauke da kayan fasinjojin

Imo - Wani al'amari mai firgitarwa ya auku a Obiohuru yankin karamar hukumar Isiala Mbano dake jihar Imo, a ranar Talata, yayin da 'yan bindiga suka tare abun hawan da ya nufi Legas suka kwashe fasinjoji.

Mota mai kirar Bas wacce ta kunshi wajen zaman mutane 14 ta baro Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a safiyar ranar inda ta nufi legas, kafin 'yan bindiga suka tsare ta.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas. Hot daga dailytrust.com
Asali: UGC

An sami labarin yadda 'yan bindiga suka tasa keyarsu zuwa wani wuri da ba a sani ba yayin da suka bar kayayyakinsu a cikin motar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, injin motar ya na aiki har zuwa lokacin da wasu matasa suka isa wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matasan ne suka sanarwa 'yan sanda.

Daily Trust ta yi kokarin kiran mai magana da yawun 'yan sandan Imo, Mike Abattam, amma bai dauki kiran ba.

A halin yanzu ana fuskantar tsananin rashin tsaro a kasar duk da cigaba da bada tabbaci daga gwamnati da jami'an tsaro.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji

A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kakakin majalisar jihar Imo, Lawman Duruji, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wakilin Punch ya tattaro bayanai akan yadda aka sace Duruji a karamar hukumar Ehime Mbano ranar Asabar a Oriagu yayin da ya ke dawowa daga wani taro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake tare babbar hanya a Arewa, sun kashe mutane sun sace wasu 40

Sun kuma yi garkuwa da wani dan kasuwa a Owerri, wanda aka fi sani da Ezzybee. A ranar Lahadi aka sace Ezzybee a hanyarsa ta zuwa wurin kallon kwallo.

Har ila yau, an sace matar wani tsohon shugaban karamar hukumar Okigwe, Frank Onwunere.

Sannan an sace wasu a daidai Okwelle da ke karamar hukumar Onuimo a cikin jihar da kuma wasu a Umbomiti da ke Mbaitili da Amaraku a karamar hukumar Mbano da ke cikin jihar.

Duk an yi wadannan sace-sacen ne a cikin jihar tsakanin ranar Asabar da Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel