Yan bindiga sun sake tare babbar hanya a Arewa, sun kashe mutane sun sace wasu 40

Yan bindiga sun sake tare babbar hanya a Arewa, sun kashe mutane sun sace wasu 40

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun tare babbar hanyar Gembu zuwa Bali dake jihar Taraba, inda suka bude wa wata mota wuta ranar Laraba
  • Rahoto ya bayyana cewa yan ta'addan sun samu nasarar hallaka fasinjoji biyu, kuma suka yi awon gaba da wasu akalla 40 a harin
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar ya tabbatar da kai harin, amma yace har yanzun hukumarsu ba ta gano adadin mutanen da harin ya shafa ba

Taraba - Da yammacin ranar Laraba, wasu yan bindiga sun tare fasinjoji a kan babbar hanyar Gembu zuwa Bali, jihar Taraba, inda suka kashe mutum biyu.

Jaridar Daily trust ta rahoto cewa yan ta'addan sun tare matafiyan a dai-dai Jamtari/ Gayam dake kan hanyar Gembu zuwa Wali, suka sace mutane.

Kara karanta wannan

Taraba: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴan tsohon SSG 6, dogarinsu da direba

Rahoto ya tabbatar da cewa maharan sun tattara akalla matafiya 40, inda suka tasa su zuwa cikin daji.

Yan ta'adda
Yan bindiga sun sake tare babbar hanya a Arewa, sun kashe mutane sun sace wasu 40 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Haka nan yan bindiga sun buɗe wa wata mota wuta yayin da take tunkaro su, wanda ya tilasta wa direbobi tsayawa.

Biyu daga cikin fasinjojin motar sun rasa rayukan su sakamakon harbin da yan bindigan suka yi wa motar da suke ciki.

Jaridar ta kuma binciko cewa yan bindigan da suka yi wannan aika-aika na daga cikin tawagar yan ta'addan da suka tsero daga jihohin Zamfara da Katsina a yan makonnin nan da suka shuɗe.

Shin yan sandan na da labarin harin?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kai harin, amma yace hukumar su ba ta gano adadin fasinjojin da maharan suka sace ba.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Kakakin yan sandan yace:

"Eh, mun samu rahoton kai harin, amma har yanzun ba mu tabbatar da adadin mutanen da yan bindigan suka yi awon gaba da su ba."

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Filato dake arewacin Najeriya yace duk yan bindigan da suka shiga hannu to kwanan su ne ya ƙare a duniya

Gwamna Lalong ya gargaɗi duk masu hannu a irin wannan harin su gaggauta barin jihar Filato ko kuma su fuskanci hukuncin kisa.

Gwamnan yace duk wani da aka cafke da hannu a garkuwa da mutane a jihar Filato, hukuncin kisa za'a zartan masa kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel