Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji

  • Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kakakin majalisar jihar Imo, Lawman Duruji a ranar Asabar da ta gabata
  • An samu bayanai akan yadda aka sace Duruji a karamar hukumar Ehime Mbano ranar Asabar yayin da yake dawowa daga wani taro
  • Har ila yau an yi garkuwa da wani dan kasuwa a Owerri, wanda aka fi sani da Ezzybee ranar Lahadin da ta gabata

Imo - Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kakakin majalisar jihar Imo, Lawman Duruji, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wakilin Punch ya tattaro bayanai akan yadda aka sace Duruji a karamar hukumar Ehime Mbano ranar Asabar a Oriagu yayin da ya ke dawowa daga wani taro.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji
Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sun kuma yi garkuwa da wani dan kasuwa a Owerri, wanda aka fi sani da Ezzybee.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

A ranar Lahadi aka sace Ezzybee a hanyarsa ta zuwa wurin kallon kwallo.

Har ila yau, an sace matar wani tsohon shugaban karamar hukumar Okigwe, Frank Onwunere.

Sannan an sace wasu a daidai Okwelle da ke karamar hukumar Onuimo a cikin jihar da kuma wasu a Umbomiti da ke Mbaitili da Amaraku a karamar hukumar Mbano da ke cikin jihar.

Duk an yi wadannan sace-sacen ne a cikin jihar tsakanin ranar Asabar da Lahadi.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abbatam ya ce yanzu haka rundunar ta fara bin sawun masu garkuwa da mutanen.

A cewarsa, ‘yan sanda sun samu nasarar ceto mutum daya daga cikin wadanda aka sace a Ubomiri.

Taraba: Ƴan bindiga sun sace ƴaƴan tsohon SSG 6, dogarinsu da direba

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun tafka barna a Zariya, sun kashe mutane sun saci dabbobi

A wani labari na daban, 'yan ta'adda sun yi garkuwa da 'ya'yan tsohon sakataren gwamnatin jihar Taraba har su shida, Gebon Kataps, tare da dan sandan da ke basu kariya da kuma direbansu.

Guardian ta ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin amma bata tabbatar da yawan wadanda aka sace ba.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan, Usman Abdullahi, ya ce lamarin ya faru wurin kauyen Jamtari da ke karamar hukumar Gashaka ta jihar.

Yayin aukuwar lamarin, 'yan ta'addan sun sheke mutum daya, wani jami'in dan sanda da ke aiki a Jamtari ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel