‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja

  • 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani direban mota mai suna Adamu Salihu tare da fasinjoji hudu a kusa da kauyen Ukya-Tsoho, karamar hukumar Kuje da ke birnin tarayya
  • Maharan sun far masu ne ta hanyar budewa motar wuta inda suka fasa tayoyin gaba lamarin da ya sa motar kwacewa direban
  • Mummunan harin ya afku ne da misalin karfe 6:32 na yammacin ranar Laraba, 5 ga watan Janairu

Abuja - Tsagerun 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani direban mota mai suna Adamu Salihu tare da fasinjoji hudu a kusa da kauyen Ukya-Tsoho, karamar hukumar Kuje da ke birnin tarayya.

Wani direba da ya tsallake rijiya da baya, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 6:32 na yammacin ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake tare babbar hanya a Arewa, sun kashe mutane sun sace wasu 40

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da direban mota tare da fasinjoji 4 a Abuja Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya ce yana tuki a bayan mota kirar Volkswagen Golf mai lamba NTT 623 XC wacce ta kwaso fasinjoji daga garin Abaji inda suka nufi Toto, lokacin da masu garkuwan suka fito daga daji sannan suka harbi motar.

Ya ce maharan sun bude wuta sannan suka fasa tayoyin gaban motar golf din inda hakan ya sa motar ta kwacewa direban sannan ya saki hanya. Nan take suka yi awon gaba da matafiyan da direban zuwa jeji.

Wani dangin daya daga cikin mutanen da aka sace, Suleiman Ibrahim, ya ce biyu daga cikin wadanda abun ya ritsa da su suna dawowa ne daga Abaji zuwa Toto a cikin wata motar haya lokacin da aka sace su.

Ya ce:

"Har zuwa lokacin nan da nake maku magana, masu garkuwa da mutanen basu kira ba, kuma babu wayar ko daya daga cikin wadanda aka sace dake shiga."

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan daba sun kai farmaki gidan talabijin, sun raunata edita tare da lalata kayan aiki

Rahoton ya kuma kawo cewa kakakin yan sandar birnin tarayya, DSP Adeh Josphine, ta nemi a bata lokaci domin yin tuntuba kan lamarin.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

A wani labari makamancin haka mun kawo a baya cewa a kalla mutane 12, ciki harda mata 10 ne aka yi garkuwa da su lokacin da yan bindiga suka kai hari kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Juma’a, 31 ga watan Disamba.

Wani jagoran matasa a garin, Jamil Kerawa, ya tabbatar da harin, yana mai cewa yan bindigar sun ci karensu ne ba babbaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel