Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa

Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa

  • Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da wani hari da yan daba suka kai wa wani jigon jam'iyyar APC mai suna Fawas Mohammed
  • Wasu yan daba da ake zaton karen farautar yan siyasa ne dai suka wanke Mohammed tare da wasu mutane uku da ruwan Acid
  • A yanzu haka daya daga cikin wadanda aka farma ya ji mummunan rauni inda yake kwance a asibitin kwararru na Yola

Adamawa - Akalla mutane hudu ciki harda wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne aka kaiwa farmaki da ruwan acid a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da harin ga yan jarida a ranar Talata, 11 ga Janairu, a Yola, ya ce an kai rahoton harin ga ofishin yan sandan Jimeta.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Nguroje ya ce wani mutum mai suna Fawas Mohammed ne ya shigar da kara a ranar 6 ga watan Janairu sannan aka fara bincike kan lamarin, Sahara Reporters ta rahoto.

Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa
Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

“DPO na ofishin yan sandan Jimeta ya sanar da rundunar jihar cewa wani Fawas Mohammed ya shigar da karar wani lamari da ya shafi kai masa da wasu uku hari da acid.
“Rundunar bayan samun korafin, sai ta bayar da umurnin bincikar lamarin.”

Sai dai, Mohammed, wani jigon APC a jihar, ya yi zargin cewa harin na da nasaba da siyasa, yayin da yake magana da yan jarida.

Mohammed ya yi zargin cewa Abubakar Sarki, jigon APC a Yola ta arewa, ne ya kitsa harin.

Mohammed ya ce:

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

“Bayan sun kai mana hari da acid a karshen Disamba 2021; yan daban sun sake kai farmaki gidana da ke unguwar Gimba, Jimeta a Yola ta arewa a ranar Juma’a, 6 ga watan Janairu da misalin 6:30 na yamma. Yan bindigar sun yi mani duka har sai da na rasa inda kaina yake sannan daya daga cikinsu ya gargadi da na daina zuwa hira da gidan radiyo sannan na daina sukar gwamnatin.”

A cewar jigon na APC, daya daga cikin wadanda aka kaima harin ya ji mummunan rauni kuma yana samun kulawar likitoci a asibitin kwararru, Yola.

Da yake martani, Sarki ya ce hukumar SSS ta gayyace shi kan lamarin, rahoton The Nation.

Ya karyata zargin Sannan ya bayyana shi a matsayin ‘bata suna’.

Sarki ya ce:

“DSS a jihar ta gayyace ni kan lamarin inda na fada masu cewa ban san komai ba kan harin da ake zargi.”

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

A wani labari na daban, mun kawo cewa gabannin babban zaben 2023, bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, ya bayyana aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa.

Kalu ya ce zai duba yiwuwar yin takarar ne idan har jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta mika tikinta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja a ranar Talata, 11 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel