Ci da ceto: Duk da yaye rufin gidansa domin ya biya kudin fansa, wasu na kokarin damfarar dattijo

Ci da ceto: Duk da yaye rufin gidansa domin ya biya kudin fansa, wasu na kokarin damfarar dattijo

  • Dattijon da ya yaye rufin gidansa don biyan kudin fansar dansa da yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Katsina ya yi karin haske kan halin da ake ciki a yanzu
  • Saidu Faskari ya ja hankalin mutane a kan masu amfani da ibtila'in da ya fada masa wajen damfarar mutane da sunansa, ya ce kudin da suka samu zuwa yanzu ya kai abun bukata
  • An dai yi zargin cewa wasu sun wallafa hoto da bidiyon dattijon sannan suka tara makudan kudi amma sai suka ki nemansa domin mika masa kudaden

Katsina - Mutumin Katsinar nan da ya yaye rufin kwanon gidansa domin ya siyar saboda ya ceto yaronsa daga hannun masu garkuwa da mutane ya ce wasu mutane sun mayar da halin da yake ciki harkar kasuwanci.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Saidu Faskari ya yaba ma yan Najeriya da suka kawo masa dauki bayan an wallafa labarinsa, amma ya ce mutane su daina aika kudi da sunansa saboda ‘an cimma adadin kudin da ake so’, Premium Times ta rahoto.

Ya yi magana ne ta hannun makwabcinsa, Ibrahim Bawa, wanda yake ta karbar gudunmawa a madadinsa.

Ci da ceto: Wasu na kokarin damfarar mutane da sunan dattijon da yaye rufin gidansa don biyan kudin fansa
Ci da ceto: Wasu na kokarin damfarar mutane da sunan dattijon da yaye rufin gidansa don biyan kudin fansa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce bayan an ceto dan Mista Saidu, mutane da dama sun aiko da kudi ta asusunsa wanda za a yi amfani da su a yanzu don tallafawa dattijon.

Mista Bawa ya ce:

“Labarin da Premium Times ta wallafa ya samu gagarumin martani kuma muna farin ciki da abun da kuka yi amma muna bukatar yin wasu karin haske.
"Ba ma son mayar da shi wani abu na daban. Ni da kaina na wallafa bidiyon saboda bani da kudin taimaka ma mutumin sannan makwabcina ne. Don haka, sai na wallafa shi don jan hankalin mutane.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Otal da sunan Kwamishinan jiha

"Mutane sun kawo agaji kuma mun yi farin ciki amma wasu mugayen mutane suna amfani da wannan bidiyo da hoton mutumin wajen yaudarar mutane. Ina so nayi amfani da wannan damar wajen kira ga jama'a da su yi watsi da duk wani rubutu da ke neman a tarawa Malam Saidu kudi.
"Yayin da muke godiya da abun da mutane suka yi, muna so mu tabbatar da ganin cewa ba a banzatar da hakan ba. Wannan mutumin na rayuwarsa shiru kuma yana son ya ci gaba a haka. Mun yi mamaki sosai da irin gudunmawar da muka samu kuma muna godiya ga kowa kan agajin da suka kawo ma mutumin."

Wani ya tara makudan kudi da sunan dattijon amma ya hana shi

Ya ce wani ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook kuma an ce ya tattara sama da N200,000 da sunan dattijon amma bai nemi iyalin ba.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

"Ba ma son kudinsa ko abun da ya tara, kawai dai muna so ya ji tsoron Allah ne sannan ya yanke daga amfani da halin da wasu mutane ke ciki. Kada wanda ya kara aika kowani kudi ga kowa da sunan Malam Saidu."

Yadda wani dattijo ya yaye rufin gidansa don ya biya kudin fansar dansa a Katsina

A baya mun kawo cewa wani manomi a Katsina, Saidu Faskari, ya cire rufin gidansa domin ya siyar yayin da yake tattara kudaden da zai biya fansar babban dansa.

Karamar hukumar Faskari na daya daga cikin yankunan da ke kan gaba a hare-haren da yan bindiga ke kaiwa yankin. Yankin na daya daga cikin wurare 13 da Gwamna Bello Masari ya datse layukan sadarwa daga cikin kokarin magance rashin tsaro.

Wani dan jarida daga Faskari, Ibrahim Bawa ya fada ma jaridar Premium Times cewa dattijon bai samu damar hada kudin fansar ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel