Zamfara: Ƴan bindiga sun sace dagacin ƙauye, wasu ƴan ƙasar waje 2 da wasu mutane 9

Zamfara: Ƴan bindiga sun sace dagacin ƙauye, wasu ƴan ƙasar waje 2 da wasu mutane 9

  • Cikin kwana 7, ‘yan bindiga sun banka wa kauyaku biyar wuta sakamakon hare-haren da su ka kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 200 duk cikin Jihar Zamfara
  • Har ila yau sun yi garkuwa da mutane 12 a kauyakun da ke karkashin karamar hukumar Anka da Bukkuyum cikin makon da ya gabata
  • Sakatare Janar na UN da shugaban kasa Muhammadu Buhari sun yi ala wadai da hare-haren da aka kai cikin takardu daban-daban

Zamfara - Cikin kwana bakwai, ‘yan bindiga sun kona kauyaku biyar inda suka kai munanan hare-hare wanda sanadin su a kalla mutane 200 sun mutu, sannan sun sace mutane 12 a wasu hare-hare biyu da suka kai jihar.

Premium Times ta ruwaito yadda kungiyoyin ‘yan ta’addan wadanda su ka kai hare-haren su ka halaka mutane 200 a kananun hukumomin Bukkuyum da Anka da ke jihar.

Kara karanta wannan

Borno: 'Yan ISWAP sun kai hari Cibiyar Yaƙi da Zaman Lafiya na Buratai, Sun halaka mutane sun ƙona motocci

Zamfara: Ƴan bindiga sun sace dagacin ƙauye, wasu ƴan ƙasar waje 2 da wasu mutane 9
'Yan bindiga sun afka Zamfara, sun sace dagajin kauye, 'yan kasar waje 2 da wasu mutane 9. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Sakatare Janar na UN da Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun caccaki hare-haren ta takardu da dama da su ka saki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mazauna yankunan sun shaida yadda harin Yar Kuka ya auku, amma wani mazaunin Anka ya sanar da Premium Times cewa sun sace wani dagacin kauye, matarsa da dan uwansa, Sarki Musa, Hadiza Musa da Bawa Musa.

Su na isa kauyen suka tunkari gidan basaraken

A ranar Litinin da dare, ‘yan bindigan sun afka kauyen inda su ka zarce gidan basaraken.

Sauran wadanda ake zargin an sace sun hada da wasu ‘yan asalin kasar Burkina Faso wadanda suke aikin hako ma’adanai da kuma wani mazaunin yankin, Dahiru Ummaru.

Harin Kadauri

Sun sace wasu mata uku da wasu ‘yan mata uku a anguwar Kuzawa da ke kauyen Kadauri karkashin karamar hukumar Maru da ke Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mummunar barna

Muhammadu Tasiu, wani dan kasuwa ya ce ‘yan bindigan sun sace matansa biyu da yaransa mata uku.

Yayin bayani ga wakilin Premium Times ta salula a ranar Talata da yamma, Tasiu ya ce maharan sun fada gidansa da misalin karfe 2:30 na dare.

Kamar yadda ya ce:

“Ina gida amma ina can bangare lokacin da su ka shigo gidan. Ba su yi ko harbi daya ba. Baya ga matana biyu da yara na mata da su ka sace, sun kwashe duk kudade na. Sunan mata na Zainab da Asmau.”

Ya ce dayar matar da suka sace makwabciyarsu ce.

Ya kara da cewa ‘yan bindigan sun kira shi amma ba su wani yi cikini da shi ba.

Kakakin ‘yan sanda ya ce bai san komai ba a kan hare-haren

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu ya ce bai san komai ba dangane da lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Kamar yadda ya shaida:

“A gaskiya ba ni da wani labari a kan hare-haren nan.”

Garkuwa da mutane tare da amsar makudan kudade, satar shanu da kashe-kashe ya zama ruwan dare a Zamfara da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel