Borno: 'Yan ISWAP sun kai hari Cibiyar Yaƙi da Zaman Lafiya na Buratai, Sun halaka mutane sun ƙona motocci

Borno: 'Yan ISWAP sun kai hari Cibiyar Yaƙi da Zaman Lafiya na Buratai, Sun halaka mutane sun ƙona motocci

  • A kalla mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin da mayakan ISWAP suka kai cibiyar yaki da kuma samar da zaman lafiya ta Tukur Yusufu Buratai, TBI
  • TBI cibiya ce ta bincike a jami’ar sojin Najeriya da ke cikin kauyen Buratai a karkashin karamar hukumar Biu a cikin jihar Borno, kuma mayakan sun kai harin ne ranar Litinin
  • Mayakan sun kai farmakin ne da yamma inda suka dinga harbe-harbe, daga nan har banka wa motoci hudu wuta su ka yi wanda hakan ya ja kowa ya fara gudun neman tsira

Jihar Borno - A kalla mutane biyu ne su ka rasa rayukansu sakamakon farmakin da mayakan ISWAP suka kai Cibiyar Tukur Yusuf Buratai ta yaki da kuma samar da zaman lafiya, TBI, da ke Jami’ar Sojin Najeriya wacce take kauyen Buratai a karamar hukumar Biu.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta musanta hannun jami'anta a fada da masu hako zinari a Katsina

Buratai shi ne asalin kauyen tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya ta kasa, kuma yanzu haka jakadan Najeriya ne a Jamhuriyar Benin, Tukur Buratai.

Borno: 'Yan ta'addan ISWAP sun halaka mutane sun kuma ƙona motocci a garin su Buratai
'Yan ISWAP sun kai hari garin Buratai, sun halaka mutane sun kona motocci. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa majiyoyi sun sanar da yadda mayakan suka afka garin ne a ranar Litinin inda su ka dinga harbe-harbe ko ta ina daga nan su ka banka wa motoci hudu wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan ya sa mutane suka dinga gudun neman tsira

Kamar yadda wata majiya daga soji ta shaida:

“Mazauna da dama sun tsere Moringa wasu kuma garin Biu. Mayakan ISWAP din sun isa garin ne da yamma rike da bindigogin harbo jiragen sama da sauran miyagun makamai.”

Yayin tsokaci akan lamarin, hukumar jami’ar sojoji ta Biu a wata takarda, ta shaida cewa fararen huluna biyu sun rasa rayukansu amma tsaro ya dawo yankin kamar da, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

Dakarun soji sun mayar wa ‘yan ta’addan hari

Kamar yadda takardar tazo:

“Yan ta’addan sun zo da yawansu inda su ka hadu da dakaru wadanda su ka matar musu da harin, hakan yasa su ka tsere. Sai dai fararen huluna wadanda ma’aikatan cibiyar ne, sun rasa rayukansu.
“Hukumar cibiyar tana yaba wa rundunar sojin bisa kokarinsu na mayar da harin kuma tana yi wa iyalan ma’aikatan da su ka rasu ta’aziyya.
“Daga karshe, hukumar na farin cikin sanar da jama’an gari cewa cibiyar ta cigaba da zama wuri mafi tsaro 100% don tuni jami’an tsaro su ka kewaye ko ina don gudun kara faruwar hakan.”

Katsina: ‘Yan bindiga sun afka Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da yaran ta 2

A wani labarin daban, ‘yan bindiga sun afka garin Makurdi da ke karkashin karamar hukumar Malumfashi a cikin jihar da daren Talata, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan bindiga sun afka Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da yaran ta 2

Sakamakon harin, mutane biyu sun rasa rayukansu sannan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wata mata da yaranta biyu.

Sun isa garin ne da yawansu don sun wuce goma kamar yadda majiyar da ta sanar da Vanguard ta shaida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel