An kuma: 'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

An kuma: 'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

  • Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun sake kai hari a Sokoto a kauyen Gatawa inda suka sace babban limami, Aminu Garba, da wasu masallata 10
  • Hakan dai yana zuwa ne bayan mummunan harin da 'yan bindigan suka kai wa matafiya a jihar ta Sokoto suka hallaka da dama ta hanyar kona su da ransu
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ya ce zai tuntubi jami'in da ke kula da yankin kafin ya yi tsokaci kan lamarin

Sokoto - 'Yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Masallaci a Neja, Sun Kashe 15 Sun Raunata Da Dama

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

An sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto
'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallaha a Sokoto. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Dan Majalisa, Sa'idu Ibrahim ya tabbatar da faruwar da harin

Dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Sabon Birni na Kudu, Sa'idu Ibrahim, ya tabbatar da harin, ya ce mutane ukun da suka jikkata suna karbar magani a babban asibitin Wamakko.

Ya ce wata mata, wacce aka harba a kauyen Dama, ta rasa kafar ta yayin da likitoci suka datse saboda an kasa gyara kafar.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ya ce zai tuntubi jami'in da ke kula da yankin sannan ya bada bayani, amma bai bada bayanin ba har lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

Tunda farko, SaharaReporters ta ruwaito cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta fatattaki yan bindiga daga kasar.

Buhari ya bada wannan tabbacin ne a ranar Juma'a a yayin da tawagar Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kai wa Gwamna Aminu Tambuwal ziyarar ta'aziyya game da kashe matafiya 23 da yan bindiga suka yi.

Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu

A baya, kun ji cewa wata mata mai shekaru 30, wacce ta tsira bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai wa matafiyan hanyar Kaduna da su ka doshi kudu ta bayyana yadda mahaifiyarta da yaranta 4 su ka kone kurmus, Daily Trust ta ruwaito.

Matar mai suna Shafa’atu, cikin matafiyan ta shaida cewa ita da yaranta, mahaifiyarta, kaninta, da yaran ‘yan uwanta su na cikin motar a wuraren titin Sabon Birni-Isa lokacin da ‘yan bindiga su ka kai musu farmaki.

Shafa’atu, wacce yanzu haka take asibiti inda ake kulawa da lafiyarta sakamakon kunar da ta yi, ta yi hira da manema labarai duk da halin da ta ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel