Ina fatan na sake ganinsa: Inji attajirin mahaifin Abdul Mutallab, wanda aka kama da bam a Amurka

Ina fatan na sake ganinsa: Inji attajirin mahaifin Abdul Mutallab, wanda aka kama da bam a Amurka

  • Alhaji Umaru Abdul Mutallab, mahaifin Farouk Abdul Mutallab, wanda aka yankewa hukuncin daurin rai-da-rai a kurkukun Amurka saboda ta'addanci ya magantu
  • Attajirin dan kasuwar ya bayyana cewa yana fatan sake ganin dan nasa a rayuwarsa
  • Ya kuma bayyana cewa su kan yi magana da dan nasa sau biyu zuwa uku a cikin wata daya

Attajirin dan kasuwa, Alhaji Umaru Abdul Mutallab, mahaifi ga Farouk Abdul Mutallab, wanda aka yankewa hukuncin daurin rai-da-rai a kurkukun Amurka saboda ta'addanci, ya bayyana cewa yana fatan sake ganin dan nasa a rayuwarsa.

Mutallab ya yi yunkurin tayar da bam wanda ya boye a cikin rigarsa a cikin jirgin Northwest Airlines Flight 253, kan hanyarsa ta zuwa birnin Detroit, Michigan daga Amsterdam, a ranar Kirsimeti, 2009.

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Ina fatan na sake ganinsa: Inji attajirin mahaifin Abdul Mutallab, wanda aka kama da bam a Amurka
Ina fatan na sake ganinsa: Inji attajirin mahaifin Abdul Mutallab, wanda aka kama da bam a Amurka Hoto: National Pilot Newspaper
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa attajirin ya bayyana muradin nasa ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu.

Da aka tambaye shi kan ko yana magana da dan nasa, attajirin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Eh, yana kiranmu a waya, wasu lokutan sau biyu, wasu lokutan sau uku a wata daya.
"Ba za mu iya kiransa ba a waya. Shi kadai ne zai iya kiranmu kuma muna magana.
"Magana ta gaskiya, mahaifiyarsa, daya daga cikin kannensa maza da daya daga cikin yan'uwansa mata sun kasance tare da shi kimanin makonni uku da suka gabata.
"Sun ziyarce shi bisa ka'idojin kurkuku mai tsanani. Amma muna ci gaba da addu'a ga Allah madaukakin sarki.
"Watakila wata rana...watakila da raina za mu gan shi ya dawo.
"Amma lamari ne da yake da daurin rai-da-rai guda uku, da kuma karin shekaru 40. Wannan da yawa.

Kara karanta wannan

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

"Amma Allah madaukakin sarki ne kadai zai kai mu yanayin ganinshi a duniyar nan, tare da 'yan uwansa a nan Najeriya."

Jaridar Punch ta rahoto cewa da aka tambaye shi kan ko yana daga cikin masu kudin Najeriya 11, tsohon ministan kuma shugaban bankin zamani ya ce ba zai sanya kansa a cikin daya daga attajiran Najeriya ba.

Ya ce:

"Ni ba talaka bane, kuma ba zan ce ina daya daga cikin mafi kudi a Najeriya ba, amma nagode wa Allah da abun da ya bani. Nagode Masa. Amma ba zan dauki kaina a cikin masu kudin Najeriya 11 ba koda da wasa ne."

A wani labari na daban, an samu tashin hankali a sananniyar kasuwar nan ta Mandate da ke garin Ilorin, jihar Kwara a ranar Talata, 4 ga watan Janairu, tsakanin wani mai saida rake da mai siya kan raken naira 50.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya zama na mutane da yawa yayin da bangarorin da ke adawa suka yi amfani da makamai.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Rikicin ya yi sanadiyar rufe kasuwar na tsawon awanni masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel