Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe mutane a Taraba, suka yiwa mazauna kashedi

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe mutane a Taraba, suka yiwa mazauna kashedi

  • Jama'a sun shiga halin fargaba a kauyen Jauro Manu na karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba sakamakon kashe mutane biyar da ‘yan bindiga suka yi
  • Maharan sun kuma yi barazanar kai farmaki wasu karin garuruwa a yankin
  • Hakan ya sanya mutane da dama yanke shawarar yin hijira zuwa yankin Mutum-Biyu, hedkwatar karamar hukumar

Taraba - Hankula sun tashi a kauyen Jauro Manu na karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba sakamakon kashe mutane biyar da ‘yan bindiga suka yi.

Hakazalika, ‘yan bindigar sun yi barazanar kai hari a wasu karin garuruwa da ke yankin.

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe mutane a Taraba, suka yiwa mazauna kashedi
Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe mutane a Taraba, suka yiwa mazauna kashedi Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa maharan, kimanin su shida sun kai farmaki garin Jauro Manu Sannan suka kashe wani Musa Iraniya, dan kasuwa kuma manomi da misalin karfe 4:30 na yanmacin ranar sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Bayan nan sai suka yi gaba suka kuma kashe wasu mazauna yankin, inda mutum biyar suka kwanta dama, jaridar Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Musa Yakubu, wani mazaunin garin ya fada ma manema labarai cewa ba a taba kai hari garin ba sai a sabuwar shekarar nan.

Ya kara da cewa sabon barazanar da ‘yan bindigar suka yi ya jefa jama’a cikin tsoro yayin da mazauna garin suke tunanin tserewa zuwa Mutum-Biyu, hedkwatar karamar hukumar.

Ya ce:

“Ankwai tashin hankali da rudani a garin. Mazauna yankin a yanzu suna rayuwa cikin tsoro.
“Mazauna yankin da dama na tunanin barin garin zuwa Mutum-Biyu don gudun hare-hare. Amma Ina so na roki hukumomin tsaro da su sake zuba ido a yankin."

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya bayyana cewa bai rigada ya samu jawabi daga rundunar yan sandan yankin ba.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Sai dai, Abdullahi ya yi alkawarin waiwayo jaridar amma bai yi hakan ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Duk yan bindigan da muka kama a jihata kwanan su ya kare, Gwamnan Arewa

A gefe guda, gwamnan jihar Filato dake arewa ta tsakiya, Simon Lalong, ya gargadi yan bindiga masu garkuwa da mutane su tattara komatsansu su bar jiharsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan yace duk wanda hukumomin tsaro suƙa kama to ba makawa zai fusakanci hukuncin kisa.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a cocin Catholic Cathedral dake karamar hukumar Shendam, a jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel