Duk yan bindigan da muka kama a jihata kwanan su ya kare, Gwamnan Arewa

Duk yan bindigan da muka kama a jihata kwanan su ya kare, Gwamnan Arewa

  • A baya-bayan nan jihar Filato ta fara fama da yawaitar hare-haren sace mutane domin neman kudin fansa
  • Gwamna Lalong ya gargaɗi duk masu hannu a irin wannan harin su gaggauta barin jihar Filato ko kuma su fuskanci hukuncin kisa
  • Gwamnan yace duk wani da aka cafke da hannu a garkuwa da mutane a jihar Filato, hukuncin kisa za'a zartan masa

Plateau - Gwamnan jihar Filato dake arewa ta tsakiya, Simon Lalong, ya gargadi yan bindiga masu garkuwa da mutane su tattara komatsansu su bar jiharsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan yace duk wanda hukumomin tsaro suka kama to ba makawa zai fuskanci hukuncin kisa.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a cocin Catholic Cathedral dake karamar hukumar Shendam, a jihar Filato.

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato
Duk yan bindigan da muka kama a jihata kwanan su ya kare, Gwamnan Arewa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya kuma tabbatarwa mazauna jihar cewa gwamnatinsa zata kara zage dantse wajen yaki da ta'addanci, musamman garkuwa da mutane wanda ya zama barazana ga zaman lafiyar al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium times ta rahoto Lalong yace:

"Zamu kara kaimi wajen kawo karshen dukkan ayyukan ta'addanci, musamman garkuwa da mutane, wanda a yanzu ya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron al'ummar Filato da wasu sassan Najeriya."

Meyasa Lalomg ya yi wannan gargadin?

Wannan gargaɗin da gwamna Lalong ya yi, ba zai rasa nasaba da harin sace mutane da ake fuskanta a wasu sassan jihar Filato ba kwanan nan.

A ranar 26 ga watan Disamba, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton sace babban basaraken garin Gindiri, dake karamar hukumar Mango, Charles Mato Dakat, a gidansa.

Amma rahoto ya bayyana cewa, maharan sun sako basaraken bayan kwashe kwanaki hudu a hannun su.

Haka nan kuma a ranar farko ta sabuwar shekara, wasu yan bindiga suka kutsa cikin gida, suka sace tsohon dan takarar gwamna, Dr Kemi Nshe, a garin Shendam.

Kara karanta wannan

Akwai abubuwa masu kyau dake jiran yan Najeriya a sabuwar shekara, Gwamna Masari

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun hallaka Basarake da wasu mutane a jihar Zamfara

Wasu miyagun yan bindiga sun kashe basarake a wani sabon hari da suka kai yankin masarautar Bungudu, jihar Zamfara.

Mazauna kauyen Gada sun bayyana cewa maharan sun cinna wuta a motocin masarauta da kuma kayan abincin da suka taras.

Asali: Legit.ng

Online view pixel